07
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fama da yunwa da wahalhalu da hauhawar hauhawar farashin kayayyaki, ƙungiyar kare haƙƙin jama'a ta Ciɓil Society Legislatiɓe Adɓocacy Centre (CISLAC) ta yi kakkausar suka ga maƙudan kuɗaɗe da shugabannin babban bankin Nijeriya CBN ciki har da gwamnanta Yemi Cardoso suka yi da mataimakansa huɗu. ƙungiyar ta sake jaddada kiran da ta yi na ɗaukar matakan gaggawa don rage tsadar harkokin mulki da kuma tabbatar da bin diddigin ayyukan gwamnati. Rahotanni sun bayyana cewa Mista Cardoso da mataimakansa, waɗanda Majalisar Dattawa ta tantance kuma ta tabbatar…
