07
Sep
Daga BELLO A BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi tsokaci game da takardar da Ƙungiyar kare Ƴancin al'ummar Musulmi (MURIC) ta fitar inda ta ce matatar man fetur ta Ɗangote na fuskantar barazana game da burinta na samar da mai a farashi mai sauƙi ga al'umma. MURIC ta tabbatar da cewa, ƙarin farashin mai da NNPCL ya yi a kwanan nan zai hana Matatar Kamfanin Ɗangote (DRL) bada man fetur a farashi mai sauƙi ga ƴan Nijeriya wanda an gina shi ne domin su amfana, wanda ta ce NNPCL ya mamaye baki ɗaya hajojin matatar. Sai dai,…
