08
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na zuba ayyuka a harkokin kiwon lafiya a jihar ganin yadda manyan asibitoci ke taka rawar gani a ɓangaren. A ranar Asabar ne gwamanan ya ƙaddamar da sake ginawa da kuma zuba kayan aiki na babban asibiti a ƙaramar hukumar Talata Mafara wanda zai ɗauki aƙalla gadojin marasa lafiya 200. Wata takarda da Kakakin gwamanan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim shi ne babban baƙo na musamman a taron. A lokacin da ya ke jawabi, gwamana Lawal ya…
