Labarai

NNPC zai kasance babban abokin cinikin matatar Ɗangote – Jami’in Gudanarwa

NNPC zai kasance babban abokin cinikin matatar Ɗangote – Jami’in Gudanarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An yi hasashen cewa kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL ne zai zama babban abokin ciniki yayin da matatar man fetur ɗin Dangote ke shirin fara fitar da mai. Matatar man Dangote ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon ƙarancin zanyen mai a baya-bayan nan, inji wani jami’in gudanarwa a ranar Litinin. Matatar mai da ta kai dala biliyan 20 a wajen birnin Legas, wanda hamshaƙin attajirin nan ɗan Nijeriya, Aliko Dangote ya gina, ta fara aiki ne a watan Janairu tare da samar da man da har zai isa a fitar…
Read More

Zagon ƙasa: Kwamitin horarwa na PDP ya karɓi rahoto kan Wike, Ortom da Makinde

Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin ladabdtarwa na Jam'iyyar PDP ya karɓi rahoton kwamitin aikace-aikace na ƙasa (NWC) game da zargin ayyukan zagon-ƙasa na Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu ƴan jam'iyyar. Kwamitin, wanda tsohon Ministan Ma'aikatar harkokin wajen, Tom Ikimi ke jagoranta, ya gayyaci Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar ne zuwa gaban jagororinsa kan zarginsu da yi wa PDP zagon-ƙasa a lokacin zaɓen 2023. Zargin ya mayar da hankali ne kan wasu gwamnonin PDP guda biyar waɗanda ake tuhumar su da yin zagon-ƙasa ga ɗan ƙarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a jam'iyyar. Gwamnonin na wancan lokacin sune; Wike -…
Read More

SERAP ta bai wa Shugaba Tinubu kwana biyu ya sauya tashin farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Ofishin tabbatar da ƴanci da adalci, SERAP ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya tsoma baki kan ƙara kuɗin man fetur da kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya yi, ya na mai nuna haramcin yin hakan da kuma bayyana shi a matsayin abu da aka yi ba bisa doka ba. Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya fitar a ranar Asabar, SERAP ya nemi shugaban ƙasa ya umarci NNPCL ya gaggauta cire ƙarin da ya yi akan farashin da ya ke a baya, kuma ya ɗauki matakin binciken rashawa a kamfanin. SERAP ya nemi Antoni…
Read More

Gwamnan Kano ya dakatar da buɗe makarantun jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da komawa makaranta ga daliban makarantun firamare da sekandire na zangon 2024/2025 bisa wasu dalilai da ba ta bayyana ba. Daraktan wayar da kan al'umma na ma'aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Ƙiru ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Ya ce, Kwamishinan Ma'aikatar, Umar Doguwa ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan matsaloli ne da ake ƙoƙarin warware su da za su taimaka wajen inganta harkar ilimi a jihar. A ranakun 8 da 9 ga watan Satumba ne aka shirya komawa makarantu don cigaba da karatu…
Read More

Tinubu ya martaba ɗalibai 462 da aka yaye a makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa kuma Kwamandan rundunar tsaro, Bola Ahmed Tinubu GCFR ya tabbatar da yaye ɗalibai 462 daga makarantar kwalejin horo ta ƴan sanda da ke Wudil a Jihar Kano zuwa sahun rundunar ƴan sandan Nijeriya. Bayan kammala shekaru biyar a makarantar su na karɓar horon karatu da na aikin ƴan sanda, an bai wa kowannen su muƙamin Mataimakin Sufuritandan ƴan sanda (ASPs). Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ya ce an gudanar da bikin yaye ɗaliban ne a filin fareti na makarantar inda masu alfarma daga ɓangarori daban-daban a Nijeriya suka halarta.…
Read More

Karɓar horon NYSC: JAMB ta buƙaci ɗaliban HND su kai kokensu ga hukumomin da suka dace

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Haɗaka ta bada Gurbin Karatu ga ɗalibai, JAMB ta shawarci ƙungiyar ɗaliban makarantun Polytechnics (NAPS), cewa ɗaliban HND da ba a tantace su ba ga tafiya hidimar ƙasa ta NYSC, su kai kokensu ga hukumomin da suka dace. A lokacin da ya ke ganawa da shugaban NAPS a hedikwatar hukumar da ke Abuja, Rijistiran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa, kamar yadda JAMB ba ita ke da alhakin bai wa ɗaliban HND gurbin karatu ba, haka kuma ba ita ce mai tantance su ba. Farfesan ya yi mamakin yadda ƙungiyar ta tunkare su da…
Read More

Ayyukan ƴan ta’adda na da alaƙa da watsi da aka yi da su – Sheikh Gumi

Daga BELLO A. BABAJI Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata iƙirarin da ake yi na cewa ƴan siyasa ke ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci a Arewacin Nijeriya. Gumi wanda sananne ne akan sharhin ayyukan ta'addanci da ke cigaba da ta'azzara a shiyyar, ya ce tashin-tashinar yankin ta na da alaƙa da watsi da aka yi da waɗansu mutane na tsawon lokaci a madadin siyasantar da al'amarin. Sanannen abu ne a ƴan shekarun nan, yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya na fama da matsalolin ta'addancin kashe-kashe da yin garkuwa da mutane ciki har da kisan Sarkin Gobir na jihar Sakkwato da aka yi…
Read More

Majalisar Shari’a ta amince ta bai wa masu zanga-zangar da aka tsare kariya

Daga BELLO A. BABAJI Darakta-Janar na Majalisar Shari'a ta Ƙasa, Aliyu Abubakar, ya tabbatar ta ƙoƙarin da su ke yi wajen bada wakilci na Shari'a ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka tsare ba tare da wani ɗauki a hukumance ba. Cikin wata hira da ƴan jarida, Abubakar ya ce kawo yanzu majalisar ba ta tuntuɓi wasu mutane ko wata kotu ba game da wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda aka tsaren yayin da ake cigaba da gudanar da shari'ar. A ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ne aka gudanar da zanga-zangar kan halin matsin rayuwa da al'umma ke ciki…
Read More

Zamfara: Bello Turji ya rage harajin da ya sanya wa Moriki zuwa miliyan N30

Daga BELLO A. BABAJI Shahararren ɗan jaridar nan, Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na X cewa an ƙulla yarjejeniya tsakanin sanannen shugaban ƴan ta'addar nan, Bello Turji da al'ummar yankin Moriki da ke jihar Zamfara. An shirya yarjejeniyar ce wadda ta ƙunshi kuɗi da za a biya kan dabbobin Turji da aka kashe. Acikin jawabin, Turji ya buƙaci Naira miliyan 50 ne da farko wanda daga baya ya rage adadin kuɗin zuwan miliyan N30. A ƙarƙashin haka, kowane magidanci zai biya N10,000 yayin da samarin da basu da aure za su biya Naira dubu biyu-biyu. Ya ce, mutanen Moriki…
Read More
Kannywood rashin jini rashin tsagawa ce – Galadima Muhammad 

Kannywood rashin jini rashin tsagawa ce – Galadima Muhammad 

DAGA MUKHTAR YAKUBU Muhammad Galadima shi ne wanda ya kula da shirin fim ɗin 'Kuka Bulukiya', wanda ya samu karramawa a taron Nigeria Week da aka gudanar a birnin Landon. Blueprint Manhaja ta tambaye shi yadda ya ji da ya samu labarin fim ɗin 'Kuka Bulukiya' ya yi nasara, sannan ko me labarin ya ƙunsa da kuma saƙon da fim ɗin ya ke isarwa? Sai ya ce, "To shi wannan fim ɗin na 'Kuka Bulukiya', ni na kasance a matsayin mai wakiltar furodusa, kuma mai kula da wajen shirya fim ɗin, sannan kuma ni na kasance a matsayin mataimakin darakta,…
Read More