23
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Tsaro ta Sibil Difens reshen Jihar Kano, ta samu nasarar kama wani mutum da ake zargin ya ƙware wajen damfarar jama’a ta hanyar karɓar kuɗaɗensu domin samar musu ayyukan yi a hukumomin jihar. Kakakin Rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano. Ibrahim Idris ya ce wanda ake zargin ya yi sojan gona, inda yake bayyana kansa a matsayin wani mai faɗa aji a jahar tare da nuna cewa yana da alaƙa da wasu hukumomin tsaro na ƙasar nan. Aƙalla dai…
