23
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin Oando ya kammala sayan kamfanin 'Nigerian Agip Oil Company' (NAOC) akan Dala miliyan 783. Kamfanin ya bada sanarwar ne a ranar Alhamis ta ofishin Satarensa, Ayotola Jagun inda ya ce hakan ya nuna cewa Oando ya zama mallakin NAOC ɗari-bisa-ɗari daga kamfanin Eni na ƙasar Italiya. Haka nan, wannan wani cigaba ne ga Oando kasancewar sa ɗaya daga kamfanonin da ke taka muhimmiyar rawa a ɓangaren samar da man fetur da gas a Najeriya. Sannan, cigaban zai taimaka wajen ƙara mamaye kaso mai tsoka a kasuwancin haɗaka da sauran kamfanoni da kuma faɗaɗa sakamakon da…
