Labarai

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙara kuɗin fasfo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar al'ummar Najeriya ƙarin kuɗin mallakar shaidar fasfo na fita ƙasashen waje. Mai magana da yawun hukumar shige da fice (NIS), DCI Kenneth Udo ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matakin na zuwa ne yayin wani yunƙuri na inganta fasfo ɗin Najeriya. A yayin kwaskwarimar da aka yi wa fasfo mai ɗauke da shafuka 32 wanda ke ƙarewa a wa'adin shekaru biyar da a ke sayar da shi a N35,000, daga yanzu, za a ke mallakar sa akan N50,000. Sai wanda ke ɗauki da shafuka…
Read More

‘Yan sanda sun kama mutane 11 bisa zargin aikata fashi da makami a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar cafke mutane 11 da ake zargi da aikata fashi da makami a cikin garin Katsina. Jami'in yaɗa labarai na hukumar ƴan sanda a jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da masu laifin inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin su, Isma'il Dawale ya jagoranci mutun biyar suka afka gidan Muntari Umar inda suka kwace masa Naira miliyan 1.85. Bayan kwana biyu ne suka sake shiga gidan wasu mata a anguwar Filin Polo inda suka raba su da…
Read More

Sarkin Gobir ya rasa ransa a hannun ƴan ta’adda bayan neman kuɗin fansa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Laraba ne aka tabbatar da rasuwar Sarkin Gobir, Isa Bawa wanda ƴan bindiga su ka yi garkuwa da shi bayan da aka gaza biyan kuɗin fansar da suka ce a kawo. Rahotanni da dama sun bayyana cewa, ƴan ta'addar ne suka kashe shi bayan ba a kai musu kuɗin da suka nema ba. Da farko dai ba'a tabbatar da rasuwar Sarkin ba sai bayan zurfin bincike da aka gudanar wanda a sakamakon haka ne gidajen jaridu suka ta ruwaitowa ciki har da BBC inda al'ummar Gobir suka shiga alhini rashin. Garkuwa da kuma kisan…
Read More

Gwamnan Zamfara ya raba tirela 135 na taki ga manoma a jiharsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata ne gwamanan Zamfara Dauda Lawal Dare, ya ƙaddamar da raba taki tirela 135 ga manoma a ƙananan hukumomi 14 na faɗin jihar. An gudanar da hakan ne a Ma'aikatar noma na jihar a ƙoƙarin gwamnan na haɓaka ayyukan noma a jihar. Wata takarda da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce buhu 81,000 kyauta ne ga manoma 40,500 a kowace ƙaramar hukuma ta jihar. Hakan kuma wani ɓangare ne na jaddada ƙoƙarin gwamnatin Dauda Lawal a Zamfara na bunƙasa harkokin noma ta hanyar tallafa wa manoma don inganta amfanin…
Read More

Shugaban NLC ya yi buris da gayyatar ƴan sanda kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero ya ƙi amsa gayyatar da rundunar ƴan sanda ta yi masa kan zarginsa da hannu a laifukan ta'addanci. Rundunar ƴan sandan ta gayyaci Ajaero ne zuwa offishinta don amsa tambayoyi game da zarginsa kan ɗaukar nauyin ta'addanci, sata ta yanar gizo da sauran su a ranar Litinin. Cikin wata takarda da tawagar lauyoyinsa ta fitar, Ajaero ya ce ba zai samu damar halartar ofishin ƴan sandan ba a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024 kamar yadda rundunar ta buƙace shi sakamakon ayyuka da su ka masa yawa,…
Read More
An cafke ɗan uwan Kwankwaso da wasu mutum huɗu a bisa kwangilar magani

An cafke ɗan uwan Kwankwaso da wasu mutum huɗu a bisa kwangilar magani

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta cafke mutane biyar waɗanda a ke zargi a badaƙalar kwangilar magani. Waɗanda a ka kama sun haɗa da Alhaji Muhammad Kabara , Sakataren Dindindin na Ma’aikatar ƙananan hukumomi da sarautar gargajiya. Akwai kuma, Alhaji Bashir Abdullahi, shine Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta Nijeriya, shugaban ƙaramar hukumar Tarauni wanda jami'in hulɗa da jama’a na hukumar ya tabbatar. Akwai shima Shugaban kamfanin Novomed Pharmaceuticals, Garba Kwankwaso, wanda ɗan uwa ne ga jagoran jami'iyyar NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso. Waɗanda a ke zargin, a na…
Read More
‘Yan China na shirin sayar da gidajen Gwamnatin Tarayya a Ingila

‘Yan China na shirin sayar da gidajen Gwamnatin Tarayya a Ingila

Masu zuba hannun jari na ƙasar China 'Zhongshang Industrial Investment' sun cigaba da shirin su na sayar da gidajen baƙi guda biyu na gwamnatin tarayya da ke birnin Liverpool a ƙasar Ingila. Masu sayarwar na shirin fara tallata gidajen a manhajar eBay in da ake hada hadar kasuwanci. Wannan dai ya biyo bayan hukunci wata kotu a Faransa, in da kamfanin ke neman gwamnatin Nijeriya da biyan kusan dala miliyan 70. Wannan ya biyo bayan wata yarjejeniya da gwamnatin jihar Ogun ta yi da kamfanin lokacin tsohon gwamnan Amosun. Duk da irin ƙoƙarin da gwamnatin Nijeriya ke yi, kamfanin ya…
Read More

NUT ta nemi mambobinta su zauna cikin shiri don nuna damuwa kan halin da shugaban NLC ke ciki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar malamai ta Ƙasa, NUT ta aika da saƙon umarni ga malamai a faɗin Najeriya kan cewa su kasance cikin shirin tafiya yajin aiki matuƙar ƴan sanda su ka kama shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero. Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sandan ta aika wa Ajaero saƙon gayyata a ranar Litinin don ya zo ofishinta a washe gari kan zargin sa da hannu acikin laifukan ɗaukar nauyin ta'addanci, zamba cikin aminci da sata ta yanar gizo inda ta ce matuƙar bai amsa kiran nata ba, to za ta kama shi. Sakamakon haka ne…
Read More

Ofishin Shugaban Ƙasa ya magantu kan matsayin jirgin Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI La'akari da sarƙaƙƙiya da ke tattare da tafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi zuwa Farisa a wani sabon jirgi mai suna A330, offishin shugaban ƙasa ya yi cikakken bayani game da jirgin. Mai taimaka wa Tinubu na musamman kan harkokin yaɗa labaran jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce jirgin ba sabo ba ne wanda an yi amfani da shi kafin ofishin ya mallake shi sannan daga baya aka saye shi ta hanyar wani banki akan tsarin sayar wa wanda ya fi biyan kaso mai tsoka daga cikin waɗanda aka tallata wa. Cikin wata hira da…
Read More
Gwamnonin hamayya da ba su raba tallafin gwamnati ba su ka assasa zanga-zanga

Gwamnonin hamayya da ba su raba tallafin gwamnati ba su ka assasa zanga-zanga

Wata ƙungiyar da ake kira 'Apostles of Jagaban' sun zargi gwamnoni daga jam'iyyun hamayya da rashin raba tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a jihohin su. Shugaban ƙungiyar, Cif Gilbert Olukususi a wata sanarwa da ya bayar ya zargi gwamnonin da karkatar da ta tallafin shinkafa da gwamnatin tarayya ta bayar domin a rabawa a al'ummar su. Shugaban ya zargi gwamnonin da rashin yin hakan, shi ya ƙara tunzura zanga-zangar matsin rayuwa da a ka gudanar a faɗin ƙasar. Ya ƙara da cewa, da irin wannan zanga-zangar su ka fake ɓatagari su ka shiga domin har su ka lalata dukiyoyin…
Read More