23
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'an tsaro na farar hula (Civil Defence) a katsina sun kama mutum uku bisa zargin su da satar wayar wutar lantarki mai amfani da hasken rana. A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun jami'in yaɗa labarai na hukumar, DSC Buhari Hamisu ya bayyana cewa cikin waɗanda ake zargin akwai Hassan Sulaiman da Jamaluddeen waɗanda ke zaune a cikin garin Katsina. DSC Buhari ya kara da cewa, hukumar ta samu nasarar kama waɗannan matasan ne a titin Usman Nagode kusa da tsohuwar ma'aikatar ayyuka inda suka aikata laifin. Su dai waɗannan matasa da jami'an suka…
