Labarai

 NGO ta koya wa mata 100 sana’o’i a Gombe

 NGO ta koya wa mata 100 sana’o’i a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI. Gombe A ƙoƙarin ta na ganin ta rage talauci ta yaƙi zaman banza a jihar Gombe, musamman a tsakanin mata, gidauniyar Motherhen Deɓelopment Foundation ta koyawa Matan karkara guda 100 sana’o'i daban-daban don su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi a wajen yaye matan da suka shafe watanni uku zuwa huɗu suna koyan sana’ar a garuruwan Shongo Idrisa Lafiya Mango da Abuja Bula a yankin ƙaramar hukumar Akko Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwalar su Asma’u Iganus, ta ja hankalin matan da cewa kar su ga sun yi abun sayarwa ba a saya ba…
Read More
 ‘Yan sanda sun kama wata mata ɗauke da bindiga da harsasai a cikin buhun gari

 ‘Yan sanda sun kama wata mata ɗauke da bindiga da harsasai a cikin buhun gari

Daga UMAR GARBA a Katsina Jami’an rundunar 'yan sanda na musamman sun kama wata mata 'yar shekara 30 mai suna Hauwa Yusuf ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da harsasan bindiga a cikin buhun garri. An damƙe matar ne a hanyar Abuja-Kaduna lokacin da jami’an rundunar 'yan sanda ke gudanar da buncike akan hanyar. Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar 'yan sandan STS da ke Abuja. Adejobi ya ƙara da cewa, Yusuf ta amsa cewa wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya yi ƙaurin suna a jihar Katsina, Aminu Basulluɓe…
Read More
Gwamnan Filato ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu hadimansa kan zargin fallasa sirri

Gwamnan Filato ya dakatar da kwamishinoni biyu da wasu hadimansa kan zargin fallasa sirri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya dakatar da wasu kwamishinoni biyu masu ci da wasu hadimansa. Mutfwang, ya sanar da dakatarwar ne a wata sanarwa da Mista Gyang Bere, daraktan yaɗa labaransa, ya fitar a ranar Talata a Jos. Ya ce gwamnan ya amince da dakatar da jami’an, ba tare da karin bayani kan dalilan ɗaukar matakin ba. Wata majiya da ke kusa da gwamnan ta shaida wa News Point Nigeria cewa an zargi kwamishinonin da aka dakatar da aika shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi zuwa ga ‘yan adawa a jihar kuma ana zargin…
Read More
Hukumar NCDC ta tabbatar da mutum 40 sun kamu da ƙyandar biri a Nijeriya

Hukumar NCDC ta tabbatar da mutum 40 sun kamu da ƙyandar biri a Nijeriya

Hukumar Kula da Cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar a ranar Juma'a cewa ƙasar ta samu mutane 40 da aka tabbatar suna da ƙyandar biri daga cikin mutane 830 da ake zargin suna da cutar. Darakta-Janar na NCDC, Dokta Jide Idris, ya sanar da hakan a taron haɗin gwiwa na NCDC/WHO na ƙasa game da ƙyandar biri tare da masu ruwa da tsaki a Abuja. WHO a Najeriya ta bayyana cewa Najeriya za ta samu alluran rigakafin ƙyandar biri kyauta daga Gwamnatin Amurka. Idris ya bayyana, “A halin yanzu, muna da mutane 40 da aka tabbatar suna da…
Read More

NYSC ta bai wa ƴan hidimar ƙasa da ƴan bindiga suka kama a Zamfara satifiket

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ta yanke shawarar bai wa wasu ƴan hidimar ƙasa satifiket bayan sun kasance a hannun ƴan bindiga tun a shekarar da ta gabata. A ranar 17 ga watan Agusta, 2023 ne a lokacin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta zuwa Sakkwato domin karɓar horon mako uku gabannin fara hidimar inda a nan ƴan bindiga suka yi garkuwa da su. Ɗaliban waɗanda su takwas ne, sun taso ne daga jihar Akwa-Ibom da ke Kudu-maso-gabashin Nijeriya a motar kamfanin jihar (AKTC) inda suka yi artabu da ƴan bindiga…
Read More

Shugaba Tinubu ya sha alwashin cigaba da samar da kayan aiki ga sojojin Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin yin amfani da ƙarfin ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi wajen tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun samu wadatattun kayan aiki domin tunkarar ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta. Shugaban ya furta hakan ne ta bakin Mataimakinsa Kashim Shettima wanda ya wakilce shi a wajen bikin yaye manyan hafsoshin soji ƴan ajin 32 da suka samu ƙarin horo kwalejin tsaron kasa a Abuja. Sanata Kashim Shettima ya ƙara da cewa, shugaban ya amince da mahimmancin samar da kyakkyawan jagoranci a matsayin ginshiƙin makamin magance matsalolin tsaro da samar da cigaban…
Read More

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Ododo na APC a matsayin gwamnan Kogi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kotun ƙoli ta tabbatar da Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023. Hakan na zuwa ne bayan da kotun ta yi watsi da ƙarar da abokin karawar sa na jam'iyyar SDP, Murtala Ajakaya shigar wanda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen. A yayin hukuncin, kotun ƙoli ta ɗora daga kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi a ranar 27 ga watan Mayu, 2024 kan batun inda a nan ma Ododo ne ya yi nasara. Tawagar masu hukunci na mutum biyar…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya rantsar da Alƙalin Alƙalan Najeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alƙalan Najeriya (CJN) ta 23 kuma mace ta biyu da ta taɓa riƙe muƙamin. Hakan ya zama mataki ne na riƙon ƙwarya kafin Majalisar Dattijai ta tabbatar da ita a matsayin ta dindindin. Ta karɓi ragamar ne daga Mai Shari'a Olukayode Ariwoola wanda ya yi murabus daga aiki a ranar 22 ga watan Agusta, 2024 wanda ke da shekaru 70 da haihuwa. Sauran bayanai za su zo daga baya.
Read More

Tinubu bai da ra’ayin mallakar OVH – Martanin NNPC ga Atiku

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗansa, Wale Tinubu wanda shi ne shugaban Kamfanin Oando, ba su da ra'ayin sayan kamfanin 'OVH Energy'. Hakan na zuwa ne bayan da tsohon Mataimakin shugaban, Alhaji Atiku Abubakar ya ce wasu ƴan ɓangaren Tinubu ne suka ƙwace kamfanin. Cikin wata sanarwa da Mai bashi Shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya bayyana yadda NNPC ta sanya wani reshenta a ƙarƙashin hukumar gudanarwar OVH wanda Oando ya mallaki kaso 49 na hannun jari acikin sa. Atiku…
Read More