Labarai

CBN ya samu ƙarin Dala miliyan 553 a watan Yuli

CBN ya samu ƙarin Dala miliyan 553 a watan Yuli

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin NIjeriya (CBN) ya samu ƙaruwar kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 553 a watan Yuli. A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun babban bankin na CBN, Hakama Sidi-Ali ta fitar, yawan kuɗaɗen da aka fi samu a duk lokacin yana nuna ƙaruwar kashi 130 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Sidi-Ali ta ce, wannan adadi ya nuna mafi girman jimillar kuɗaɗen da ake samu a kowane wata kuma ya nuna ƙoƙarin babban bankin na ci gaba da haɓaka kuci a kasuwar canji ta Nijeriya. A cewarta, babban ci gaban…
Read More
Majalisar ƙasa ta musanta amincewa da salon mulkin Tinubu – Rahoto

Majalisar ƙasa ta musanta amincewa da salon mulkin Tinubu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani labari na baya-bayan nan ya ci karo da kalaman da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ ya yi tun farko, inda ya yi iƙirarin cewa Majalisar ƙasa (NCS) ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da salon mulkin Shugaban Nijeriya Bola Tinubu a yayin taron farko da ta yi a makon jiya. Gwamna AbdulRazaƙ, wanda kuma ke riƙe da muƙamin Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), a baya ya bayyana cewa NCS da NGF tare sun nuna amincewarsu ga salon mulkin Shugaba Tinubu. "Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a taron majalisar shi ne amincewa da salon mulkin shugaba…
Read More
Bashir Hadejia ya yi ƙaryar naɗa shi muƙami – Gwamnatin Zamfara

Bashir Hadejia ya yi ƙaryar naɗa shi muƙami – Gwamnatin Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Laraba ya musanta naɗa wanda ake zargin ɗan ta’adda ne kuma ɗan bindiga, Bashir Hadejia, a matsayin mataimaki na musamman a gwamnatinsa. An kama Hadejia ne a ranar Litinin ɗin makon jiya bisa zargin cin amanar ƙasa da zagon ƙasa ga jihar. Wanda ake zargin dai shi ne mai ba wa Aaramin Ministan Tsaro na ƙasa, Bello Matawalle shawara na musamman a lokacin yana Gwamnan Jihar Zamfara. Bayan kama shi, wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 27 ga Oktoba, 2023, wacce aka ce sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Mal…
Read More
Zaɓe a Kano: NNPP ta buƙaci ciyamomi da kansiloli da ke muradin tsayawa takara su yi murabus

Zaɓe a Kano: NNPP ta buƙaci ciyamomi da kansiloli da ke muradin tsayawa takara su yi murabus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar NNPP a Kano ta ba wa dukkan shugabannin riƙon ƙwarya da kansiloli a ƙananan hukumomi 44 da ke kan gaba su yi murabus har zuwa ƙarshen wannan wata. Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a Kano ta haƙura har zuwa ƙarshen wannan wata ga dukkan shugabannin riƙo da kansiloli a ƙananan hukumomi 44 da su yi murabus. “Waɗanda suke da muradin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe, su yi murabus daga naɗin nasu,” in ji jam’iyyar. Shugaban Jam’iyyar Hashimu Dungurawa ne ya bayar da wannan umarni a lokacin da…
Read More
Kotu ta aike da mai shagon magani gidan yari bisa yi wa yarinya fyaɗe har ta mutu

Kotu ta aike da mai shagon magani gidan yari bisa yi wa yarinya fyaɗe har ta mutu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Kotun Majistare a Kano da ke zamanta a unguwar No-man’s-land a Sabon Gari, ta bayar da umarnin a tsare wani mai shagon saida magani (Chemist) a gidan yari bisa zargin yi wa wata yarinya 'yar shekara tara fyaɗe. Lauyan jiha, Barista Zainab Aliko, ta shaida wa kotun cewa, ana tuhumar mai shagon saida maganin, Manniru Ibrahim Fanisau da yi wa marigayiyar, Rumaisa Sadik fyaɗe, a lokacin da aka kawo masa ya duba ta saboda tana fama da Maleriya. Barista Aliko ta ƙara da cewa a sakamakon lamarin yarinyar ta mutu. Wanda ake tuhumar…
Read More
 ‘Yan sanda sun kama masu satar waya 35 a Kaduna

 ‘Yan sanda sun kama masu satar waya 35 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dangane da karuwar aikata laifuka a baya-bayan nan, musamman satar waya, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna mai yaki da masu garkuwa da mutane ta kai samame tare da cafke wasu mutane 35 da ake zargi da satar wayar. Daga cikin wadanda ake zargin akwai mata biyu da maza 33, wadanda dukkansu an gurfanar da su a gaban kotu. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce an gudanar da aikin ne tsakanin karfe 19:00 zuwa 23:45, yana bin umarnin kwamishinan ‘yan sanda. A cewar ASP Hassan, “an kai farmakin ne kan gano…
Read More
Hisbah ta kama kwalaben barasa 24,000 a Kano

Hisbah ta kama kwalaben barasa 24,000 a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wata mota maƙare da kwalaben barasa sama da 24,000 a kan titin BUK da ke Jihar. Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujaheed Aminudden ne, ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Talata. Ya bayyana cewa an kama motar ne ranar Litinin da tsakar rana a daidai lokacin da ta ke ƙoƙarin shiga cikin gari. Kazalika, ya bayyana cewa dokar hukumar Hisbah ta haramta sayarwa da shan barasa da sayar kayan maye a jihar. Ya ce hukumar ta ƙudiri aniyar wayar wa al’umma…
Read More
Yadda aka ƙone ɓarayin adaidaita sahu har lahira a Bauchi 

Yadda aka ƙone ɓarayin adaidaita sahu har lahira a Bauchi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu fusatattun matasa sun ƙone wasu mutum biyu har lahira, bayan an zarge su da kashe wani matuƙin adaidaita sahu tare da sace babur ɗinsa a ƙaramar Hukumar Misau a Jihar Bauchi. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kisan wani matashi mai shekara 25, Muhammad Mamuda Baba Jibir. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Wakil ya ce, “Eh, an samu laifukan haɗin baki, fashi da makami, da kuma kisan kai. A ranar 18 ga watan Agusta, 2024, da misalin ƙarfe 10 na dare,…
Read More
 Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci Yahya Bello ya miƙa kansa gaban EFCC

 Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci Yahya Bello ya miƙa kansa gaban EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta umarci Yahya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi da ya gabatar da kansa gaban hukumar EFCC domin gurfanar da shi gaban kotu. Kotun ta warware hukuncin babbar kotun jiha dake Kogi ta yi na hana EFCC kama Yahya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi ta Naira biliyan 80. A wani hukunci na bai ɗaya da kotun ta yanke a ranar Talata, alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Ken Amadi ta dakatar da  Yahya Bello daga ɗaukar wani mataki game da tuhumar da ake masa har sai an…
Read More
 Muna fuskantar ƙalubale a jagorancin kasuwar gwarin Illeoko a Legas – Mu’awuya Simoli

 Muna fuskantar ƙalubale a jagorancin kasuwar gwarin Illeoko a Legas – Mu’awuya Simoli

Daga DAUDA USMAN a Legas  Wani babban mai faɗa a ji a kasuwar gwarin Illeoko ta ƙaramar Hukumar Alimosho dake cikin birnin Ikko, Alhaji Mu'awuya Idris Simoli ya bayyana cewar shi da sauran shuwagabannin kasuwar ta gwarin Illeoko suna fuskantar manyan ƙalubale mai yawa a kasuwar da kewayenta gaba ɗaya. Alhaji Mu'awuya Idris Simoli ya furta hakan ne a Legas a lokacin da yake zantawa da jaridar Blueprint Manhaja dangane da al'amuran da suka shafi harkokin kasuwancin gwari a Legas baki ɗaya. Simoli ya ci gaba da labarta wa Jaridar Blueprint Manhaja cewar haƙiƙa tun daga wancan lokacin ya zuwa…
Read More