Labarai

Za mu haɗa kan Arewa da samar wa yankin mafitar siyasa – Shekarau

Za mu haɗa kan Arewa da samar wa yankin mafitar siyasa – Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata sabuwar ƙungiya ta wasu gogaggun ‘yan siyasa a Arewacin Nijeriya, ta ce ta fara lissafin samar da mafita ga yankin. Wasu da suka kira kansu masu kishin arewacin Nijeriya sun ɓullo da sabon yunƙurin ne da nufin sama wa yankin ingantaccen shugabanci da alƙibla ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa. Sun kira wannan yunƙuri nasu da taken ''League of Northern Democrats'', a turance - wani taron dangi na wasu masu faɗa a ji na arewacin Nijeriya, da suka haɗa da tsofaffin gwamnoni da ma'aikatan gwamnati da 'yan siyasa da tsofaffin sojoji…
Read More
Gwamnatin Jigawa ta raba wa marasa galihu buhuna 59,000 na kayan abinci

Gwamnatin Jigawa ta raba wa marasa galihu buhuna 59,000 na kayan abinci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da ake ka-ce-na-ce tsakanin Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi dangane da abincin da Gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi, ita kuwa Jihar Jigawa ta ƙaddamar da rabon kayan abincin da ta karɓa daga hannun tarayya ɗin. Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ƙaddamar da rabon kayan abincin a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, wanda ya ƙunshi buhuna 59,000 na shinkafa mai nauyin kilo 25, masara da sauran kayan abinci. An fara rabon ga marasa galihun yau da kullum a mazaɓu 287 da ke faɗin jihar. Da yake jawabi a Dutse lokacin rabon…
Read More
Tsohuwar minista, Ezekwesili ta caccaki Gwamnatin Tinubu kan sayen sabon jirgin Shugaban ƙasa

Tsohuwar minista, Ezekwesili ta caccaki Gwamnatin Tinubu kan sayen sabon jirgin Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta yi zargin cewa fadar shugaban ƙasa da majalisar dokokin ƙasar sun yanke shawarar zama 'yan fashi da makami a Nijeriya. Daily Trust ta rawaito cewa Ezekwesili ta bayyana hakan ne a lokacin da take tsokaci kan siyan sabon jirgin shugaban ƙasa, yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na Channels Tɓ’s Politics Today. Ta ce an sayi jirgin a yayin da 'yan Nijeriya na shiga ƙara shigewa cikin ƙangin talauci duk minti ɗaya. Ezekwesili ta ce, “A duk abin da muka ji, suna cewa wai tsohon…
Read More
ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano

ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta kulle asusun bankin kamfanin Novomed Pharmaceuticals saboda binciken da ake yi kan badaƙalar magunguna a Jihar Kano. Ana binciken wata kwangila da Ma’aikatar Harkokin ƙananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kano, ta bayar ga kamfanin don samar da magunguna ga ƙananan hukumomin jihar 38. Ana zargin cewa an karya dokokin saye da sayarwa na gwamnati wajen bayar da kwangilar. Wata majiya daga ICPC, wadda ta nemi a sakaya sunanta, taa bayyana cewa matakin da hukumar ta ɗauka na da nufin hana zurarewar kuɗaɗen da aka…
Read More
An saka ranar fara sayar wa matatar man Ɗangote da ɗanyen mai a Naira

An saka ranar fara sayar wa matatar man Ɗangote da ɗanyen mai a Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alamu dai na nuna cewa 'yan Nijeriya sun kusa samun sauƙi yayin da ake sa ran fara sayar da ɗanyen mai ga matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida a ranar 1 ga Oktoba, 2024. Masu fashin baƙi sun ce sayar da ɗanyen mai ga matatun man ƙasar nan a Naira zai rage farashin man fetur ɗin sosai. A cewar wani saƙo da aka wallafa a shafin ɗ na ma’aikatar kuɗi, sanarwar ta fito ne daga ganawar da ministan kuɗi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya yi da kwamitin…
Read More
Takardu sun nuna ɗan uwan ​​Ɗangote na cikin masu shigo da fetur daga Malta

Takardu sun nuna ɗan uwan ​​Ɗangote na cikin masu shigo da fetur daga Malta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An samu ƙarin bayanai kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da su ke da hannu wajen shigo da man fetur marasa inganci daga Malta, inda Sayyu Dantata, ɗan uwa ga shugaban rukunin Dangote Aliko Dangote na ɗaya daga cikin masu shigo da kayan. A watan Yuli, Dangote ya yi zargin cewa wasu jami’an kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPC da dillalan mai suna haɗa masana’antun mai a Malta, inda suke tacewa da shigo da kayayyakin da ba a taɓa gani ba, waɗanda ake kawowa Nijeriya domin amfani da su. Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da…
Read More
An kashe ɗalibar jami’a da aka yaudara da Naira 15,000

An kashe ɗalibar jami’a da aka yaudara da Naira 15,000

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An tsinci gawar wata budurwa mai suna Mojisola Awesu, ɗalibar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara. Budurwar mai shekara 21 da aka bayyana ɓacewarta tun ranar 9 ga watan Agustan 2024, an same ta babu rai a wani wajen zubar da shara da ke unguwar Aleniboro a Ilorin, babban birnin jihar. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata. Kakakin rundunar, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa marigayiyar ta samu kiran waya daga wata Mis Timileyin a ranar 9 ga watan Agusta, 2024, game da wani taron da ɗaliban makarantar a Offa, da…
Read More
Hukuma ta rufe wani kamfanin ruwa a Abuja

Hukuma ta rufe wani kamfanin ruwa a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMAMD Hukumar da ke kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki da abokan hulɗa ta ƙasa, FCCPC, ta rufe kamfanin ruwa na Fabsi da ke Kubwa, Babban Birnin Tarayya, biyo bayan ƙorafin da masu amfani da shi suka yi na amfanin da lalatattun robobi masu ɗauke da ƙwayoyin cuta. Hukumar, a hukumance ta shafinta na ɗ ranar Juma'a, ta ce bincikenta ya gano gagarumin keta ƙa'idojin kariya na masu amfani da kamfanin. FCCPC ta ce, Fabsi ya gaza samar da muhimman bayanai, gami da kwanan watan samarwa, kwanakin ƙarewa, da lambobin batch a kan samfuran nasa. Hukumar ta…
Read More
Naira miliyan 29 ta yi wa sanatoci kaɗan saboda ’yan maula – Sanata Abbo

Naira miliyan 29 ta yi wa sanatoci kaɗan saboda ’yan maula – Sanata Abbo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Sanata Elisha Abbo, wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya ce, Naira miliyan 29 da sanatoci ke karɓa duk wata, ba kuɗi ne da suka taka kara suka karya ba idan aka yi la’akari irin ɗimbin maular da ake yi musu. Ya ce, lokacin da yake sanata, yana samun Naira miliyan 14.4 a wata, amma yanzu ’yan Majalisar Dattawa suna karɓar Naira miliyan 29. Abbo, ya bayyana cewa, kuɗaɗen ba za iya biyan buƙatun sanata ba, domin shi talaucewa ya yi a lokacin da ya ke Majalisar Dattawa. Ya ƙara da cewa,…
Read More
’Yan bindigar Nijar sun kashe sojojin Nijeriya huɗu a Sakkwato

’Yan bindigar Nijar sun kashe sojojin Nijeriya huɗu a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarun rundunar ‘OPERATION HADARIN DAJI’ sun yi arangama da wasu 'yan bindiga a yankin dajin Bachaka Kurya da ke ƙaramar Hukumar Gudu a Jihar Sakkwato a ranar 10 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 11:45 na rana, inda suka rasa jami’ai huɗu. Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata, ya ce an yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar. Ya ce, a yayin da ake gwabzawar ɓarin…
Read More