Labarai

Sarkin Gobir: ACF ta buƙaci a zurfafa bincike da sauya matakan tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar mashawarta na Arewa, ACF tayi watsi da kisan gillar da aka yi wa Alhaji Isa Muhammad Bawa, Sarkin Gobir na Sabon Birni wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da kashe shi a jihar Sakkwato. Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 18 ga watan Agusta ne aka yi garkuwa da Sarkin tare da ɗansa inda aka buƙaci kuɗin fansa wanda duk da ƙoƙarin da aka yi na samar da abin da suka buƙata, sai da suka azabtar tare da kashe shi. Cikin wata sanarwa daga Taskar Gizago, ACF ta bayyana rashin jin daɗinta game da al'amarin…
Read More

Shettima ya umarci sojoji su tsaurara matakan kariya na ƙalubalen tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya umarci rundunar jami'an sojin Nijeriya da su kasance masu lura da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen tunkarar matsalolin tsaro da ke shiyyoyinsu. Shettima ya yi kiran ne a lokacin bikin yaye ɗaliban sojoji na Kwalejin Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NDC) a Kwas na 32 a Abuja. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron, ya ce gwamnatinsu na da burin mayar da Nijeriya waje mai tsaro don zuba hannun-jari da samar da nasara ga tattali. Ya kuma yi tsokaci game da buƙatar shugabanci mai salo na magance rashin…
Read More

Gwamnatin Katsina ta ƙaryata umarnin ƴan jiha su mallaki makamai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta bayar da umarni ga ƴan jihar su mallaki makamai don kare kawunansu daga hare-haren ƴan bindigar daji a faɗin jihar. Da ya ke hira da manema labarai a ofishinsa, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dakta Nasir Mu'azu, ya ce gwamnati ba ta bayar da umarni ga ƴan ƙasa fararen hula su mallaki makamai domin yaƙar ƴan ta'adda ba. Maimakon haka gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki jami'an tsaro na al'umma 7,000 waɗanda tuni bayan samun horo aka tura su ƙananan hukumominsu, domin tunkarar ƴan ta’addar.…
Read More

Haukan gado ya sa wata mata ta ƙone kanta a Jigawa

Daga Umar Aƙilu Majeri a Dutse Kamar yadda binciken ƴan sanda ya tabbatar, sun gano cewa ciwon haukan gado ne ya sa wata mata mai kimanin shekaru 40 mai suna Fatsuma Bagobiri ta banka wa kanta wuta a ƙauyen Garin Mallam da ke Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce, an samu rahoton faruwar lamarin ne a safiyar ranar Alhamis da ta gabata kuma jami’an ofishin ƴan sanda na shiyyar Guri sun gaggauta kai wa matar ɗauki a lokacin da…
Read More

Gundogan ya sake dawo wa Manchester City

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar Manchester City ta ƙasar Ingila ta sake ɗaukar ɗan wasa Ilkay Gundogan daga ƙungiyar Barcelona. Ɗan wasan na ƙasar Jamus ya rattaɓa hannu a kwantiragin shekara ɗaya bayan ya bar ƙungiyar a shekarar 2023. Gundogan mai shekaru 33 yayi nasarar lashe kufuna 12 cikin shekaru bakwai da yi a zangonsa na farko a matsayin ɗan wasan Man City ciki har da firimiyar Ingila guda biyar da kuma kofin zakarun Nahiyar Turai guda ɗaya a shekarar 2023. Ɗan wasan ya ce ya ji daɗin kasancewar sa a Manchester City a halin fafatawa da kuma akasin haka…
Read More

Tinubu ya naɗa Sanata Barau shugaban kwamitin raba kayan tallafi na Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin a matsayin shugaban kwamitin shugaban ƙasa na raba kayan tallafin rage raɗaɗin talauci ga al'ummar jihar Kano. Sanata Barau ya faɗi haka ne a wani zama inda ya ce kasancewar ana zargin sauya akalan wasu kayayyakin tallafi na al'ummar Kano ya sanya aka ƙirƙiri sabon kwamitin. Ya ce, kwamitin na da wakilci daga jam'iyyun APC, PDP da NNPP da majalisar mashawarta na jam'iyyu (IPAC) da kuma sarakunan gargajiya. An yi da zaman ne musamman kan yadda za a gudanar da raba tallafi ga…
Read More

NELFUND ya samu ƙarin biliyan N50 daga EFCC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ofishin asusun bada aron kuɗin karatu ga ɗalibai, NELFUND ya samu shaidar ƙarin kuɗi da adadinsa ya kai Naira biliyan 50 daga hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC). 'News Agency Nigeria' ya ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa ofishin Naira biliyan 60. Daraktar yaɗa labarai ta NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi ta faɗi haka acikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a. Ta ce kuɗin da EFCC ta bayar ya biyo bayan umarni ne da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar a ranar 4 ga watan Agusta don a bunƙasa shirin bada aron…
Read More

Tinubu ya sha alwashin inganta dokar ƙasa da sauƙaƙe adalci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyarsa ta cigaba da inganta kiyaye dokar ƙasa da sauƙaƙe shugabanci na adalci a Nijeriya. Tinubu ya faɗi haka ne a lokacin bikin rantsar da sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ta riƙon ƙwarya, Kudirat Kekere-Ekun a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shugaba Tinubu ya bayyana yadda gwamnatinsa ke ƙoƙari wajen saduakarwa ga kiyaye dokar ƙasa tare da tabbatar da an bai wa ɓangaren alƙalanci goyon bayan da ya ke buƙata saboda matsayin muhimmancin sa a wajen al'ummar ƙasa da zaman lafiyar su. Ya yi kira ga Kekere-Ekun ta tsare aikinta…
Read More