26
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan ma'aikatar Ilimi, Tahir Mamman ya ce ba za a sake barin ɗaliban da shekarunsu ya gaza ba su rubuta jarrabawar kammala sekandire. Ministan ya faɗi haka ne a lokacin da ake hira da shi a tashar telebijin na 'Channels' inda ya ce gwamnatin tarayya ta umarci ofisoshin kula da jarrabawar ɗaliban sekandire na yammacin Afirka (WAEC) da ke bayar da shaidar WASSCE da kuma na jarrabawar Ƙasa (NECO) da ke shirya SSCE su tabbatar ɗalibi ya kai shekaru 18 kafin a bashi damar rubuta ɗaya daga cikin jarrabawar. Sannan ya nanata cewa, game da jarrabawar…
