Labarai

Wata ƙungiyar Saudiyya ta kai Euro miliyan 65 don sayen Osimhen

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Ahli da ke ƙasar Saudiyya ta kai tsabar kuɗi har Euro miliyan 65 wa Napoli don sayen ɗan wasanta na gaba, Victor Osimhen. Ana ganin Osimhen wanda ɗan wasan Super Eagles ta Nijeriya ne, zai bar ƙungiyarsa ta ƙasar Italiya a wannan kakar. A ranar Lahadin da ta gabata ba a shigar da shi sahun ƴan wasan da suka fafata ba da ƙungiyar Bologna ba. Rahotanni sun bayyana cewa, babu wata yarjejeniya tsakanin ɗan wasan da Al Ahli duk da cewa Napoli ta yarje masa ficewa daga gare ta. Kawo yanzu…
Read More

Tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson ya mutu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Litinin ne tsohon kocin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila, Sven-Goran Eriksson ya mutu ya na da shekaru 76 bayan fama da rashin lafiya ta cutar daji. Kocin wanda ɗan asalin ƙasar Sweden ne ya jagoranci ƙungiyar ƴan ƙwallon Ingila ne a tsakanin shekarun 2001 da 2006 inda ya yi nasarar kai ƙasar zuwa zagayen wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar kofin duniya na 2006. A watan Fabrairun shekarar 2023 ne ya ajiye ayyukan da suka shafi harkar ƙwallon ƙafa sakamakon matsaloli na kiwo lafiyarsa.
Read More

NYSC ta bada damar sauya wurin hidima ga matan aure

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da ɗalibai masu hidimar Ƙasa, NYSC ta bai wa matan aure da aka tura su jihohin da ba a nan mazajensu suke ba dama ta su nemi a sauya mu su jiha. NYSC ta fitar da sanarwar ne ta shafinta na kafar X inda ta ce matan za su je sansanin hukumar mafi kusa tare da takardunsu don a canja mu su zuwa wajen da su ke so su yi hidimar. Ta ce, da zarar an gama sauya wa mutum inda ya nema, zai ga hakan a shafinsa na hukumar. An samar da NYSC…
Read More

An samu gawar Kwamishinan Kuɗi na Borno a ɗakinsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A safiyar ranar Litinin ne aka samu gawar Kwamishinan Kuɗi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed a ɗakinsa. Rahotonni sun bayyana cewa an gano cewa mamacin ya wuce lokacin da ya saba fitowa ne da safe wanda hakan ya sa aka ɓalle ƙofar dakin nasa inda aka same shi a mace. Wannan shine mutum na biyu da gwamna Babagana Zulum na jihar ya rasa ɗaya daga cikin muƙarrabansa a wannan shekarar.
Read More

NNPC ya faɗaɗa kasuwancinsa na gas zuwa Japan da Chana

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI La'akari da ƙoƙarin yin fintinkau a ɓangaren samar da ingantaccen mai, kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya fara shigar da gas na ruwa (LNG) zuwa ƙasashen Japan da Chana ta tsarin kai wa ta tashar jiragen ruwa da aka yi yarjejeniya akan ta (DES). NNPC yayi nasarar haka ne ta haɗin gwiwa da rassansa na tace albarkatun mai, wato NNPC LNG Ltd. da NNPC Shipping LNG waɗanda suka fara kai ɗiban farko na LNG a tsarin DES zuwa ƙasar Japan a ranar 27 ga watan Yuni 2024. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun…
Read More
Likitoci sun shiga yajin aikin gardaɗi na kwana bakwai

Likitoci sun shiga yajin aikin gardaɗi na kwana bakwai

Ƙungiyar likitoci ta ƙasa sun shiga yajin aiki a faɗin ƙasa wanda zai fara daga 12am na 26 ga Agusta, 2024. Babban dalilin shiga yajin aikin shine domin kira ga gwamnati a saki Dr Ganiyat Popoola wadda ke tsare yau wata takwas. Shugaban ƙungiyar Dr Dele Abdullahi shi ya bayyana yajin aikin bayan fitowa daga wani taron gaggawa na majalisar ƙungiyar. Sauran bayanai za su biyo…
Read More
Mashaƙo ta kashe yara uku a Zaria

Mashaƙo ta kashe yara uku a Zaria

Wata tawagar ma'aikata daga ma'aikatar lafiya ta Jihar Kaduna da kuma hukuma lafiya ta duniya sun tabbatar da mutuwar yara uku sanadiyar cutar mashaƙo a anguwar Tukur Tukur da ke ƙaramar hukumar Zaria, Jihar Kaduna. Tawagar ta samu jagorancin Dakta Jamo, wanda shine shugaban hukumar lafiya ta matakin farko a Jihar kaduna a yayin ziyarar domin tabbatar da lamarin. Dakta Jamo ya bayyana cewa anguwar Tukur Tukur na ɗayan daga cikin wurare da su ka ƙi amsar rigakafi lokacin da ake yi. Ya roƙi mutanen anguwar da su rinƙa amincewa da rigakafi domin kare yaransu da kansu daga wannan muguwar…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sallami Bichi, ya naɗa sabbin shugabannin DSS da NIA

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sallami Bichi, ya naɗa sabbin shugabannin DSS da NIA

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Adeola Oluwatosin Ajayi a mastayin sabon shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) Ajayi zai maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda shine shugaban hukumar tun lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Sannan ya naɗa Ambasada Muhammad Muhammad a matsayin shugaban hukumar leƙen asiri na Nijeriya bayan murabus ɗin tsohon shugaban Ahmed Rufai. Wannan sanarwar ta fito daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara a fannin yaɗa labarai Ajuri Ngelale.
Read More

‘Yan sandan da aka kashe: Kun farar da yaƙi a tsakaninmu – Kwamishinan ƴan sandan Abuja ga ƴan Shi’a

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igweh ya bayyana rashin jin daɗinsa game da kashe wasu jami'ansu guda biyu da aka yi a yayin wani zagaye na mambobin Shi'a. Ya bayyana hakan a matsayin salo na fusatarwa wajen kai hari ga jami'an tsaro wanda hakan bai bar wasu mata guda biyu ba da aka raunata a yayin aukuwar lamarin a Abuja. Rahotanni sun nuna cewa an harbe wani ɗan kasuwa har lahira tare da kashe ƴan sanda biyu a lokacin da aka yi artabu tsakanin ƴan sanda da ƴan Shi'a tare da ƙone motocin ƴan sanda uku…
Read More

Kwanaki kaɗan da kisan Sarkin Gobir, ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum 150 a Gobir

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Aƙalla mutane 150 tare da dabbobi guda 1,000 ne ƴan bindiga suka yi garkuwa dasu a wasu ƙauyuka da ke yankin Masarautar Gobir a jihar Sakkwato. Hakan ya faru ne a ƙasa da kwanaki uku da kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa da ƴan bindiga suka yi bayan sun yi garkuwa da shi wanda kuma shi ne Hakimin Gatawa. Bayan haka ne aka samu wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ga Sarkin an ɗaure masa ƙafafu da hannaye ya na magiya ga gwamnatin Sakkwato, Fadar Sarkin Musulmi, ƴan uwansa da…
Read More