Labarai

Allah ya yi wa wakilin Jaridar Manhaja, Muhammed Ali, rasuwa a Gombe

Allah ya yi wa wakilin Jaridar Manhaja, Muhammed Ali, rasuwa a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe A ranar Talata da ta gabata, Allah ya yi wa wakilin jaridar Manhaja a jihar Gombe, Muhammed Ali, rasuwa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Marigayin, wanda ya rasu yana da shekara 70, ya bar matar aure daya da ’ya’ya takwas. Muhammed Ali, tsohon dan jarida ne wanda ya shafe tsawon shekarunsa yana aikin jarida. Haifaffen garin Jos ne a jihar Filato, asalin Kanuri daga garin Dikwa a jihar Borno. An haife shi a ranar 10 ga watan Janairu, shekarar 1955. Marigayin ya halarci Makarantar Firamare ta Nur-Ud-Deen dake garin Jos daga shekarar 1960…
Read More
Taɓargaza: Mai shayi ya sheƙe matashi saboda taliya da madara a Jigawa

Taɓargaza: Mai shayi ya sheƙe matashi saboda taliya da madara a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Tafaru ta ƙare a wani shagon sayar da shayi inda mai shayin ya yi anfani da wani ƙaton itace ya sheƙe wani matashi saboda yana zarginsa da sace masa kayan shayi a unguwar Jigawar Tsada da ke Ƙaramar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa Ana zargin mai sayar da shayin ya yi ta dukan matashin da itace ne har sai da ya daina yin nunfashi saboda wai yana zargin ya sace taliyar indomi a shagonsa da yake sana,ar sayar da shayi a unguwar Jigawar Tsada ta Jihar Jigawa. Wannan mummunan lamari ya faru ne a…
Read More
Surukar Nuhu Ribaɗo ta rasu

Surukar Nuhu Ribaɗo ta rasu

Surukar Nuhu Ribaɗu, Hajiya Ummu Iya Abubakar ta rasu a safiyar Talata a Abuja. Iyalan Farfesa Iya Abubakar ne su ka sanar da rasuwar. An yi jana'izar ta da ƙarfe 1:30 a masallacin ƙasa da ke Abuja. Za a rufe ta maƙabartar Gudu da ke cikin Abuja.
Read More

Hukumar NAPTIP ta ceto yarinya yar shekara 7 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar hana fataucin bil'adama ta Ƙasa reshen jihar Katsina ta samu nasarar ceto yarinya da aka kaita aikatau a birnin Abuja tun tana da shekaru 7 da haihuwa. Wata takardan sanarwar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar na jiha, Musa Aliyu Haɗeja ya ce yarinyar ƴar ƙaramar hukumar Malumfashi ne a jihar Katsina. Ya bayyana cewa, hukumar ta miƙa yarinyar ga iyayenta tare da bata tallafi na kanya ɗinki domin ta koyi sana'a. Alhaji Aliyu Haɗeja yayi kira ga iyaye suyi ƙoƙarin bai wa ƴaƴansu ilimi da tarbiyya mai kyau da kuma koya mu su…
Read More

‘Yan sanda sun kama masu yi wa ƴan bindigar Katsina, Kaduna da Zamfara safarar makamai

Daga Umar Garba a Katsina Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargin suna kai wa masu garkuwa da mutane makamai a jihohin Kaduna, Katsina da kuma Zamfara. Kakakin rundunar, Mansir Hassan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai. "A ranar 24 ga Ogasta, 2024 jami’an ƴan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane da ke ta'addanci a jihohin Kaduna, Katsina da kuma Zamfara". Inji Sanarwar." Kakakin, ya ƙara…
Read More

Gwamnatin Tinubu za ta rufe gidajen mai masu tsauwala wa kwastomomi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ofishin hukumar kula da tace man fetur ta Ƙasa, NMDPRA ta aika saƙon gargaɗi ga gidajen man fetur da ke tsananta wa kwastomomi inda wasu ke sayar da lita a farashin da ya kai Naira 1,000. Hukumar ta zargi wasu ƴan kasuwa masu zaman kansu da ke ɓata ƴan Nijeriya ta hanyar sayar da lita ɗaya a tsakanin Naira 900 zuwa 1,000 wanda ya haura kuɗin da ƙasa ta ƙayyade. Hakan ya haifar da koke-koke acikin al'umma wanda ya kai ga samun cinkoso a gidajen mai da dama a Nijeriya. La'akari da yadda…
Read More
Al’adarmu ta Arewa ba ta gamsu da ganin mace tana ƙwallon ƙafa ba – Aisha Kissar

Al’adarmu ta Arewa ba ta gamsu da ganin mace tana ƙwallon ƙafa ba – Aisha Kissar

  Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Aisha Kissar wata matashiya ce a Jihar Kano, wacce ta kasance ɗaya daga cikin tsirarun mata masu sha'awar ƙwallon ƙafa tun tana yarinya. Wani abu da ya ƙara sa Aisha ta zama daban da sauran 'yammata shi ne duk da yadda take son ƙwallon ƙafa ba ta wasa da sha'anin karatu, na boko da na addini, don yanzu haka tana da haddar rabin Alƙur'ani a kanta. Kuma duk da cewa tana son harkar wasannin motsa jiki, amma ba ta bari son zuciyarta ya shiga tsakaninta da iyayenta ba, waɗanda suke nuna wasan ƙwallon ƙafa bai…
Read More

Tinubu ya yi alƙawarin sauraron mabambantan ra’ayoyi – Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙudiri aniyar samar da ci gaba wajen kiyaye dokar ƙasa da bin tsarin mulkin karɓa-karɓa gami da sauraron mabanbanta ra'ayoyi da dokar Nijeriya ta amince da su. Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi, ya faɗi haka ne a taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) na shekara-shekara da aka yi a Legas. Ya ce, gwamnatinsa tun farawarta, ta samu gagarumar nasara wajen sabonta ƙasa ta fuskar doka da gyare-gyaren tsare-tsarenta. Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa ƙungiyar a ƙoƙarinta na jagorantar kundin demokraɗiyya da kuma kiyaye bin doka da oda…
Read More
Bruno Labbadia ya zama sabon kocin Super Eagles

Bruno Labbadia ya zama sabon kocin Super Eagles

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta sanar da cewa sun sami matsaya da mai horar wa ɗan asalin ƙasar Jamus Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin Super Eagles. Sakataren hukumar Dakta Muhammed Sanusi shi ya bayar da wannan sanarwa a safiyar Talata. Labbadia an haife shi a shekarar 1966, Fabarairu. Ya yi nasarar cin kofi biyu lokacin yana ɗan wasa a ƙungiyoyin Darmstadt 98, Hamburger SV, FC Kaiserslautern, Bayern Munich, FC Cologne, Werder Bremen, Armenia Bielefeld da Karlsruher SC. A matsayin koci, ya jagoranci ƙungiyoyi irin su, VfL Wolfsburg, Hamburger SV da Bayer Leverkusen. Ga yadda jadawalin Kocin Super Eagles…
Read More