Labarai

Ɗangote ya sauko daga mataki na mafi kuɗi a Afrika

Ɗangote ya sauko daga mataki na mafi kuɗi a Afrika

Ɗangote ya sauko daga matakin wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka biyo bayan Johann Rupert da ya wuce shi da jimillar kuɗi Dala biliyan 13.65. A wani rahoto da Bloomberg su ka fitar na masu kuɗin duniya, Rupert ya kasance a mataki na 154 inda ya wuce Ɗangote da mataki biyu. Wannan rahoton ya nuna cewa Ɗangote ya yi asarar Dala biliyan 10 a cikin watanni shida wanda ya janyo jumullar kuɗin shi su dawo Dala biliyan 13.6 inda Rupert ya wuce shi da Dala miliyan 50. Wannan saukowa da Ɗangote yayi za a iya danganta shi irin matsin…
Read More

Tinubu zai gabatar da ƙudirin tsarin fallasa ɓarayin gwamnati ga majalisa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A kwanan nan ne Shugaba Tinubu zai gabatar da ƙudirin tsarin fallasa ɓarayin gwamnati ga Majalisar Ƙasa don ɗaukar mataki daga gare ta. Ministan Kuɗi kuma ministan shirya Tattali, Wale Edun ya faɗi hakan a Abuja a lokacin wani zama da aka yi wa laƙabi da 'Implementing the whitselblowing policy in Nigeria issues, challenges and the way forward.' Ya ce, gwamnatin tarayya ta na buƙatar taimakon ƴan Nijeriya wajen sanya tsarin ya yi aiki ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci. Edun yace tsarin fallasar na daga cikin salo da gwamnati ta ɗauka wajen tabbatar da…
Read More

Za mu cire Nijeriya daga jaddawalin ƙasashe masu fuskantar barazanar kuɗi na FATS, inji Gbajabiamila

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya zata ɗauki matakin cire Nijeriya daga cikin jadawalin ƙasashe masu fuskantar barazanar tattali na FATF kafin watan Mayu na shekarar 2025. Shugaban ma'aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ya bada tabbacin hakan a wani ziyarar bincike da ya kai ofishin cibiyar leƙen asiri na harkar kuɗin Nijeriya, NFIU a Abuja inda ya ce gwamnatin tarayya zata yi ƙoƙarin warware matsalolin da suka sa ta kasance ɗaya daga ƙasashen jadawalin. Gbajabiamila ya bayyana haka ne bayan da Darakta-Janar kuma shugabar NFIU, Hafsat Bakari ta nemi a gaggauta kai wa matakin da FATF ta zayyana acikin…
Read More

An kama ƴan fashi kan zargin sojan-gona na ƴan sanda

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumomin kiyaye doka na jihar Legas sun kama wasu mutane biyu da ake zargin su da fashi sanye da kayan ƴan sanda a yayin wani atsaye a jihar. Wani ɗaukar bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ƴan sanda suka gurfanar da waɗanda ake zargin ɗauke da makamansu da wasu ababe da ke nuna cewa ƴan fashi ne inda wanda aka jiyo muryar ɗaukar ta na cewa sun sanya kayan ƴan sandan ne da ke ɗauke da muƙaman Sufeto don fashi ga mazauna jihar. Kawo yanzu babu wani saƙo daga rundunar ƴan…
Read More

Ba don ƙananan masana’antu ba, da kaso 80 na ƴan Nijeriya ba su da aikin yi – Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yace kashi 80 na ayyukan yi ya ta'allaƙa ne sakamakon yaɗuwar ƙananan masana'antu (MSME) acikin al'umma a Nijeriya wanda rashin hakan ka iya haifar da rashin aikin yi ga wannan kason. Shettima ya faɗi haka ne a Markudi, babban birnin jihar Benue a lokacin buɗe gidan kayan ƙawa na jihar da hukumar buga takardu da wallafa su ta jihar (BPPC) inda ya ce ƙananan masana'antu ginshiƙi ne ga tattalin arziƙin ƙasa don haka gwamnatin shugaba Tinubu ke ƙoƙarin haɓaka su. Ya ce, abu ne mai wahala tattalin arziƙin Nijeriya ya samu…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta tara N60b daga cire tallafin taki – NSIA

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Litinin ne Hukumar kula da harkokin Zuba hannun-jari ta Ƙasa, NSIA ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 60 a ɓangaren cire tallafin taki a ƙarƙashin shirin taki na shugaban ƙasa (PFI) cikin shekaru takwas. Hukumar, wadda tayi nazari kan ayyukan PFI, ta ce hakan wani yunƙuri ne bunƙasa masana'antar takin Nijeriya inda aka samar da masarrafa guda 84 a shiyyoyi shida na Nijeriya. Ci gaban ya kuma tara Dala miliyan 200 daga hada-hadar cinikayyar ƙasashen wajen wanda hakan ya taimaka wajen samar da ayyuka 100,000. Hakan nan, shirin PFI ya…
Read More
WHO na buƙatar Dala miliyan 87.4 domin yaƙar cutar ƙyandar biri

WHO na buƙatar Dala miliyan 87.4 domin yaƙar cutar ƙyandar biri

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa ta na buƙatar Dala miliyan 87.4 a tsawon wata shida domin yaƙar cutar ƙyandar biri a ƙasashe. Hukumar ta bayyana cewa wannan kuɗin ta na buƙatar su ne domin auwatar da wasu ayyuka da za su taimaka wajen daƙile yaɗuwar cutar mai mugun haɗari. Wannan yana ƙunshe ne a cikin jadawalin agajin gaggawa da hukumar ke shirin bayarwa ga ƙasashe da ke fama da annobar. Hukumar na kira ga masu taimakawa da su kawo agaji domin su fara yaƙin cutar da gaggawa a ƙasashen da ke fama da annobar cutar.
Read More
Har yanzu babu lokacin aiwatar da rahoton Orunsaye – Gwamnatin Tarayya

Har yanzu babu lokacin aiwatar da rahoton Orunsaye – Gwamnatin Tarayya

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila wanda shine tsohon kakaakin majalisar wakilai ya sanar da cewa babu lokacin aiwatar da rahoton Orunsaye. Femi ya sanar da haka ne a yayin wata tattaunawa da yayi lokacin da ya kai ziyara hukumar NEITI a Abuja.Ya ce gwamnatin tarayya na iya ƙoƙarin ganin cewa an samu aiwatar da babu matsala a tare da ita. In ba mu manta ba, a watan Fabarairu, majalisar zartaswa ta ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta bada umarnin aiwatar da rahoton Orunsaye wanda ya ƙunshi soke wasu ma'aikatun gwamnatin tare da haɗe wasu domin ragewa…
Read More

NERC ta bai wa jihohi shida ƙarfin gudanar da harkokin lantarki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar gudanar da wutar lantarki ta Ƙasa, NERC ta bai wa jihohi shida ƙarfin gudanar da kasuwancin lantarkin yankunansu a wani yunƙuri na samar da ci gaba a harkar ƙasuwancin lantarki. Cikin wata sanarwa da hukumar ta sanya a shafinta na X, ta ce ta bai wa jihohin Enugu, Ekiti, Ondo, Imo, Oyo da Edo lasisin gudanar da harkokin kasuwancin lantarkinsu. Hakan na zuwa ne bayan da jihohin suka samar da hukumomin gudanar da lantarkinsu wanda hakan ya ba su matsayin kula da ɓangaren a yankunansu. NERC ta bayyana cewa, ci gaban ya samu ne bisa…
Read More

Tinubu zai gana da shugaban Chana kan tattalin arziƙi a Beijing

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya shirya haɗuwa da shugaban ƙasar Jamhuriyar Chana a birnin Beijing wanda za a yi a satin farko na watan Satumba, kamar yadda mai magana da yawunsa, Cif Ajuri Ngelale ya faɗa. Za a yi ganawar ne kan batun muhimman ababen harkar tattali da suka haɗa ƙasashen biyu inda za a shirya takardar yarjejeniya wanda aciki akwai; 'green economy' da 'blue economy' da kuma shirye-shiryen Ƙasa. Kawo yanzu ba a faɗi takamaiman ranar da Shugaba Tinubu zai bar Nijeriya ba. Cif Ajuri ya ce Shugaba Tinubu zai tattauna kan manyan batutuwa da shugaban…
Read More