Mutum shida sun mutu sakamakon arangamar ‘yan shi’a da ‘yan sanda a Abuja

Spread the love

Mutum shida sun mutu a sanadiyar wata arangama tsakanin ‘yan shi’a da ‘yan sanda a cikin babban birnin tarayya a Abuja.

‘Yan sanda biyu na cikin waɗanda su ka rasa rayukansu da wasu da dama da su ka jikkata.

Hargitsin ya fara ne a lokacin da mabiya shi’a su ka kai wa ‘yan sandan da ke hanyar Wuse hari. A cewar rundunar ‘yan sandan mabiyan sun fito da muggan makamai irin su wuƙaƙe, adduna da kuma ƙananan bama-bamai da a ke haɗawa da kalanzir.

Arangamar ta haifar da ƙonewar motocin sintiri na ‘yan sanda da wasu motocin da ke kusa da wurin.

‘Yan sanda sun bada rahoton cewa yanzu sun sami damar dawo da doka da oda a wurin.

Mai magana da yawun ‘yan sandan babban birnin tarayya Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar haka, ta bayyana cewa ƴan sanda biyu sun mutu yayin da wasu guda uku suka jikkata da motocin sintiri uku da aka ƙona.

Kwamisshinan ‘yan sandan babban birnin ya bayyana cewa, sun kama aƙalla mutum 52 waɗanda za su gurfanar gaban kotu da zarar an gama bincike.

By ukarofi