27
Aug
Ƙungiyar kansiloli ta ƙasa, wato National Progressive Councilor’s Forum (NPCF), ta buƙaci a naɗa shugabanta Hon Muslihu Yusuf Ali a muƙamin Minista a Gwamnatin Tarayya. A cewar ƙungiyar ta ce ta ayyana Muslihu don naɗa shi minista ne biyo bayan sanar da sake Ministan Matasa da Shugaba Bola Tinubu ya yi ba tare da ya bayyana da ko wane ne ba. NPCF ta bayyna haka ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Agusta, 2023 da kuma sa hannun Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Hon Abayomi kazeem. A cewarta, "La'akari da sanarwar da Fadar…
