Labarai

Ban goyi bayan yaƙar Nijar ba — El-Rufai

Ban goyi bayan yaƙar Nijar ba — El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gargaɗi Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS da ta dakatar da shirin ɗaukar matakin soji a Jamhuriyar Nijar. El-Rufai da ya ke bayyana dalilin da ya sa ya ke jan hankalin ECOWAS da ta yi taka-tsan-tsan, ya ce yan Afirka ‘yan uwan ​​juna ne, kuma yakin da ake yi a kowace ƙasa zai yi illa ga kowa. El-Rufai ya bayyana hakan ne ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya sunansa Tiwita ya bayyana cewa ‘yan ƙasar Nijar da ‘yan…
Read More
Kotun Birtaniya na tuhumar Diezani kan zargin cin hanci

Kotun Birtaniya na tuhumar Diezani kan zargin cin hanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya a kotu, kan laifukan cin hanci. Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci. Ranar 2 ga watan Oktoba, Diezani Madueke za ta bayyana a gaban Kotun Majistare ta Westminster. Tun bayan kamun da aka yi mata na farko a London cikin watan Oktoban 2015, Diezani Alison-Madueke ta ci gaba da zama a matsayin beli. Jim kaɗan bayan kama…
Read More
Gwamnatin Tinubu za ta fitar da ‘yan ƙasa miliyan 133 daga talauci — Sabuwar Minista

Gwamnatin Tinubu za ta fitar da ‘yan ƙasa miliyan 133 daga talauci — Sabuwar Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabuwar ministar harkokin jinƙai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu ta bayyana ƙudirin gwamnatin tarayya na fitar da 'yan Nijeriya miliyan 133 daga ƙangin talauci. Edu ta bayyana hakan ne a lokacin da ta fara aiki a ranar Litinin a Abuja tare da gudanar da taron gaggawa da manyan jami’an ma’aikatun da ke ƙarƙashin ma’aikatar. Ta kuma tabbatar wa 'yan Nijeriya aniyar ta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a zaman ta a matsayin minista. Ta yi bayanin cewa, ma’aikatar za ta cimma burinta ta hanyoyi daban-daban da tsare-tsare da nufin fitar…
Read More
Ba za mu yi ƙarya don kare muradun gwamnati ba – Ministan Labarai

Ba za mu yi ƙarya don kare muradun gwamnati ba – Ministan Labarai

Daga BASHIR ISAH Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Muhammad Idris Malagi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa ba ta buƙatar sharara ƙarya don kare muradun gwamnati, "za mu riƙa faɗin komai yadda yake", in ji shi. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki bayan rantsar da shi da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi a ranar Litinin. Ya ce ma'aikatarsa da gwamnati za su zama masu gaskiya wajen bada bayanai. Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta kasance mai ƙoƙarin yin gyara a duk inda ta yi kuskure. Haka nan, ya ce nan ba da daɗewa…
Read More
Rundunar ‘yan sanda ta haramta zanga-zanga a Kano gabanin yanke hukuncin zaɓen gwamna

Rundunar ‘yan sanda ta haramta zanga-zanga a Kano gabanin yanke hukuncin zaɓen gwamna

Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta haramta kowane irin nau'i na zanga-zanga a faɗin jihar. Da yake sanar da wannan doka a jihar a ranar Litinin, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Husaini Gumel, ya ce dokar ta fara aiki nan take. A cewar Kwamishinan, bayanan sirri sun nuna jam'iyyun NNPP da APC a jihar na shirin gudanar da zanga-zanga dangane da zaman kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar. Idan ba a manta ba, Jam'iyyar APC a Kano ta shigar da ƙara kotu inda take ƙalubalantar bayyana NNPP da hukumar zaɓe INEC ta yi a matsayin wadda ta lashe…
Read More
DSS ta cafke Manajan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

DSS ta cafke Manajan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Hukumar tsato ta DSS ta tsare Manajan Jirgin ƙasan a Abuja-Kaduna na Kaduna, Pascal Nnorli, biyo bayan takardar sanarwar gargaɗin yiwuwa kai wa jirgin hari da ta bayyana. Majiya mai tushe daga Hukumar Jirgin Ƙasa ta Nijeriya ta shaida wa jaridar News Point Nigeria an tsare Manajan ne tare da Manajan Ayyuka na hukumar, Victor Adamu da kuma wasu ma'aikatan hukumar. Blueprint Manhaja ta rawaito a makon jiya DSS ta yi gargaɗin tsaro ga hukumar inda ta ce ta bankaɗo shirin 'yan bindiga na yiwuwar kai harin kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna kowane lokaci. Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun…
Read More
FUGA Gashuwa ta yi sabbin mataimakan Shugabar Jami’ar

FUGA Gashuwa ta yi sabbin mataimakan Shugabar Jami’ar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Hukumar Zartaswar Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa a Jihar Yobe (FUGA) a, taronta na 44 a ranar Jummu'a, a ƙarƙashin shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta amince da naɗin Dokta Ibrahim Ahmed Jajere da Dokta Mohammed Attai Yakubu a matsayin Mataimakan Shugabar Jami’ar; na ƙwararru da na sha'anin gudanarwa. A cikin wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Malam Adamu Saleh ya fitar ta ce, Hukumar Zartaswar ta amince da naɗin mataimakan shugabar jami’ar guda biyu ne a ƙarƙashin doka Sashe na 4 na dokokin Jami’o’i mai lamba 11 na shekarar 1993,…
Read More
An zaɓi Nasiru Mera a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai na ɗaya

An zaɓi Nasiru Mera a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai na ɗaya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ƙungiyar Izala da ke da shalkwata a Kaduna reshen Ƙaramar Hukumar Mulki ta Argungu da ke Jihar Kebbi ta zaɓi Malam Nasiru Abubakar Mera a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai na 1. Shugaban majalisar malaman Sheikh Suleman Bawa ya bayyana cewa zaɓen Malam Nasiru Abubakar Mera ya biyo bayan la'akari ne da irin gudummawar da ya ke bayarwa wajen da'awa da kuma sauran hanyoyi wajen yaɗawa da ɗaukaka addinin Musulunci. Sabon mataimakin shugaban majalisar malaman ya jaddada cigaba da bayar da duk gudummawar da ya yi wajen ɗaukaka addinin Musulunci tun kama daga da'awa ya…
Read More
Sanata ya raba taki har da ‘yan adawa a Kebbi

Sanata ya raba taki har da ‘yan adawa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin shirinsa na samar da taki don sauƙaƙa wa manoma raɗaɗin wahalar noma, Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar mazaɓar gundumar Kebbi ta Arewa ya raba takin zamani a mazaɓarsa. Da ya ke jawabi jiya Alhamis a wajen ƙaddamar da rabon takin, Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Kebbi Alhaji Usman Bello Suru ya bayyana cewa Sanata Yahaya Abubakar Mallamawan Kabi ya umarci a bai wa kowa ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba saboda wakilcin da ya ke yi ba na al'ummar PDP kaɗai ba ne. Haka zalika yana da tabbacin ba 'ya'yan…
Read More
Gwamna Buni ya rantsar da sabbin kwamishinoninsa

Gwamna Buni ya rantsar da sabbin kwamishinoninsa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rantsar da sabbin kwamishinoninsa 20 tare da ma'aikatunsu daban-daban, inda ya umurce su da bin ƙa'idar aikin. Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban ɗakin taron da ke gidan gwamnatin jihar a Damaturu. Gwamna Buni ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe tare da Mambobinsa bisa gaggauta tantance sunayen kwamishinonin, ya ce hakan ya nuna kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalisa don kawo ci gaban al'ummar jihar Yobe. Haka kuma, Gwamnan ya taya sabbin kwamishinonin murna bisa naɗa su Kwamishinoni kuma mambobin Majalisar Zartarwar jihar.…
Read More