19
Aug
Daga JOHN D WADA a Lafiya Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin yi wa ‘yan mata masu shekaru tsakanin shekara 9 zuwa 14 rigakafi domin kare su daga kamuwa da cutar sankarar mahaifa da ta mama. Dokta Mohammed Addis, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Nasarawa, NPHDA, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi ranar Alhamis a Lafiya. Ismaila Oko, Manajan Shirye-Shirye, Cibiyar Kula da Rigakafi na Gaggawa ta Jiha ne ya wakilci shugaban a wajen taron. Dokta Addis ya bayyana cewa jihar Nasarawa na cikin jihohi 16…
