Labarai

Tsare Emefiele: DSS ta yi amai ta lashe

Tsare Emefiele: DSS ta yi amai ta lashe

Hukumar tsaro ta DSS ta bayyana cewa, dakataccen Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, yana hannunta. Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar, Peter Afunanya, shi ne ya sanar da haka a ranar Asabar. Sanarwar da jami'in ya fitar ta ce, “DSS ta tabbatar da Mr Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), yanzu yana hannunta." Sanarwar ta kuma buƙaci jama'a, musamman 'yan jarida da su lura da yadda suke ba da rahoto. Da fari DSS ta ƙaryata rahoton da aka yaɗa cewa hukumar ta tsare Emefiele sa'a guda bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da shi.
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Emefiele ba ya hannunmu – DSS

Da Ɗumi-ɗumi: Emefiele ba ya hannunmu – DSS

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS ta musanta cewa tana tsare da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, kamar yadda aka yaɗa da farko. Da fari rahotannin da aka yaɗa a kafafe mabambanta sun nuna hukumar tsaro (DSS) ta cika hannu da Emefiele jim kaɗan bayan aka sanar da dakatar da shi daga matsayinsa a ranar Juma’a. Sai dai da yake mayar da martani ga rahoton, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya bayyana a ranar Asabar cewar, “A yanzu dai Emefiele ba ya hannun DSS.” A ranar Juma’a Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin…
Read More
Zulum ya bada umarnin binciken ma’aikatan asibitin da suka ƙi karɓar waɗanda suka yi haɗari

Zulum ya bada umarnin binciken ma’aikatan asibitin da suka ƙi karɓar waɗanda suka yi haɗari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umurci ma’aikatar lafiya da ta yi bincike tare da kamo ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki bisa zargin ƙin amincewa da waɗanda hatsari ya rutsa da su a asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da ke Maiduguri. Zulum ya bayar da umarnin ne a ranar Alhamis a sashin bada agajin gaggawa na asibitin.Ziyarar da gwamnan ya kai asibitin Umaru Shehu na zuwa ne a matsayin martani ga wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ke nuna yadda wasu jami’an kiwon lafiya suka ƙi…
Read More
Tinubu ya sa hannu kan dokar tsawaita aikin alƙalai zuwa shekaru 70

Tinubu ya sa hannu kan dokar tsawaita aikin alƙalai zuwa shekaru 70

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattava hannu kan ƙudirin dokar da ke neman tsawaita wa’adin ritayar alkalan babbar kotun ƙasar daga shekaru 65 zuwa 70. Shugaban Ƙasa ya amince da ƙudirin dokar shekarun ritayar alƙalan Babbar Kotun ƙasar rana Alhamis, 8 ga Yuni, 2023. A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Abiodun Oladunjoye, Daraktan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, ya ce Tinubu ya sanya hannu kan dokar “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Fifth Change) (No. 37), 2023,” wanda Majalisar Ƙasa ta 9 mai barin gado ta gabatar da shi.…
Read More
Emefiele ya faɗa a komar DSS sa’a guda bayan dakatar da shi

Emefiele ya faɗa a komar DSS sa’a guda bayan dakatar da shi

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS ta tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, bisa zargin ta'addanci. Wannan na zuwa ne ƙasa da sa'a guda bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, dakatarwar da Shugaba Tinubu ya yi wa Emefiele daga ofishinsa ta fara aiki ne nan take. Kamar dai yadda sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ta nuna a ranar Juma'a.
Read More
Nijeriya za ta ci gaba idan aka zuba jari mai yawa wajen ilimin ‘ya’ya mata – NPC

Nijeriya za ta ci gaba idan aka zuba jari mai yawa wajen ilimin ‘ya’ya mata – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana cewa Nijeriya za ta iya samun gagarumin ci gaba idan aka zuba jari mai yawa a Shugaban Hukumar Ƙidaya na Ƙasa, Hon. Nasir Isa Kwarra, shi ne ya bayyana haka a yayin da hukumar ta shirya wani taron gabatar da rahoton yawan jama'a na ƙasa kamar yadda ta saba yi a duk shekara, a Birnin Tarayya Abuja. A jawabinsa da farko, Hon. Kwarra ya nuna matuƙar farin cikinsa tare da yi wa baƙin da suka halarci taron maraba, inda ya bayyana cewa taron ya tattara su ne don ƙarin haske game da…
Read More
Kwamishinan Bauchi ya ba Tinubu shawara kan cire tallafin man fetur

Kwamishinan Bauchi ya ba Tinubu shawara kan cire tallafin man fetur

*Ya ce ya kafa kwamiti don gano badaƙalar da ke NNPC Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wani tsohon Kwamishinan Ilimi a Jihar Bauchi, Dokta Aliyu Usman Tilde ya shawarci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kafa wani kwamiti wanda zai gano ainihin kuɗaɗen tallafin man fetur da ƙasar nan ke buƙata daga yawan man fetur da 'yan ƙasar ke amfani da shi yau da kullum. "Ka jingine shaci-faɗin alƙaluma da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da qwararru 'yan baranda masu neman cusa maka karkatattun ra'ayoyi. Ka ƙaddamar da asalin naka bincike da zummar gano gaskiyar tallafi da ƙasar…
Read More
Gwamnan Neja ya rushe ofishin ’yan sandan da aka gina kan bututun ruwa

Gwamnan Neja ya rushe ofishin ’yan sandan da aka gina kan bututun ruwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Umaru Bago, ya rusa ofishin ’yan sanda na Chanchaga da ke Minna, Babban Birnin Jihar ta Neja. A cewar wata sanarwa da mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa na zamani, Abdullberqy Ebbo, ya fitar, ta ce, an gina ofishin ’yan sandan ba bisa ƙa’ida ba a kan wani babban bututun ruwa. Idan dai za a iya tunawa, gwamnan a yayin jawabinsa na ƙaddamar da ayyuka, ya sha alwashin rusa ofishin ’yan sandan, saboda kawo cikas ga samar da ruwan sha a babban birnin jihar. Ebbo ya ce, ofishin…
Read More
An buƙaci mazauna yankin Mabushi su bai wa hukumar VIO haɗin kai

An buƙaci mazauna yankin Mabushi su bai wa hukumar VIO haɗin kai

Hakimin Mabushi da ke yankin Abuja, Alhassan Mabushi, ya ziyarci Ma'aikatar Kula da Harkokin Hanyan da Ababen Hawa, wato FCT Directorate of Road Traffic Services. Yayin ziyarar tasa, Basaraken ya yaba wa Shugaban ma'aikatar, Dr AbdulLateef Bello dangane da shigar da shirin karɓar lambar motoci da inshora a intanet don kawar da wahalar da jama'a kan fuskanta wajen karɓar lamba. Hakimin ya yi amfani da wannan dama wajen kira ha al'ummarsa na yankin Mabushi da su bai wa ma'aikatar cikakken goyon game da ayyukanta. Tawagar da ta yi wa Hakimini rakiya ta ƙunshi tsohon Kodinetan Cibiyar Bunƙasa Garuruwan Gefen Abuja,…
Read More
Zan yi bakin ƙoƙari wajen kawo cigaba a ɓangaren kasuwar tattasai a Legas – Aminu Musa

Zan yi bakin ƙoƙari wajen kawo cigaba a ɓangaren kasuwar tattasai a Legas – Aminu Musa

Daga DAUDA USMAN a Legas Sabon shugaban kulawa da cigaban kasuwancin tattasai, atarugu da shambo a Kasuwar Mile 12 dake Legas, Alhaji Aminu Musa, ya bayyana cewar zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajen kawo cigaban kasuwancin tattasai, tarugu da shambo a Legas. Alhaji Aminu Musa ya yi wannan tsokaci ne a ofis ɗin sa dake kasuwar Mile-12 a Legas a lokacin da yake karvar baƙuncin waɗansu daga cikin 'yan kasuwar waɗanda suka zo taron walimar taya shi murnar zama sabon shugaban ɓangaren tattasai, tarugu da shambo. Aminu ya ce yana yi wa kowa fatan alheri dangane da wannan al'amari, da fatan…
Read More