Kwamishinan Bauchi ya ba Tinubu shawara kan cire tallafin man fetur

*Ya ce ya kafa kwamiti don gano badaƙalar da ke NNPC

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Wani tsohon Kwamishinan Ilimi a Jihar Bauchi, Dokta Aliyu Usman Tilde ya shawarci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya kafa wani kwamiti wanda zai gano ainihin kuɗaɗen tallafin man fetur da ƙasar nan ke buƙata daga yawan man fetur da ‘yan ƙasar ke amfani da shi yau da kullum.

“Ka jingine shaci-faɗin alƙaluma da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da qwararru ‘yan baranda masu neman cusa maka karkatattun ra’ayoyi. Ka ƙaddamar da asalin naka bincike da zummar gano gaskiyar tallafi da ƙasar nan ke buƙata daga haƙiƙanin alƙaluma na yawan man fetur da al’ummar ƙasa ke amfani da shi yau da kullum.”

Dokta Aliyu Tilde, a cikin wata buɗaɗɗiyar takardar shawara da ya gabatar wa Shugaba Tinubu dangane da buƙatar sake yin dubi kan batun janye tallafin man fetur da ya fitar a waɗannan kwanaki, ya ce duk wata gwamnati tagari takan yi tallafi wa jama’arta kan lamuran rayuwarsu, gwargwadon ƙarfin ta bisa ƙarfin tattalin arzikin jama’a.

“Ka kafa wani kwamiti wanda zai ƙunshi nagartattun mutane masu kyawawan halaye da ƙwarewa, waɗanda kwata-kwata ba su da nasaba da kamfanin man fetur na NNPC daga sassan ma’aikatu masu zaman kansu, jami’o’i da ƙungiyoyin qwadago su gano ainihin yawan man fetur da ƙasar nan ke sanarwar da yawan wanda take amfani da shi.”

Tilde, wanda ya ajiye aikinsa na Kwamishina a ƙarƙashin gwamnatin Jihar Bauchi mai ci, watanni huɗu gabanin zaɓen gamagari na ƙasa, bisa amintakarsa da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi da’awar a bai wa kwamiti daya shawara ta a kafa kimanin sati uku, wanda rahoton wucin-gadin sa zai bai wa shugaban ƙasa mahangar tudun dafawa kan cire tallafin man fetur.

Ya bayyana cewar, kwamitin bayan ya bayar da rahoton wicin-gadi, za a saka masa ƙarin wa’adi na watanni biyu domin ya bai wa Shugaban Ƙasa sahihan alƙaluma da za su kasance madogara a gare shi, yana mai cewa, wannan ba zai kasance mawuyacin umarni ba daga wajen shugaban ƙasa.

“Zuwa ƙarshen wannan wata na Yuni, Shugaba Tinubu zai aike wa majalisun dokoki na tarayya ƙarin kasafi na wannan lokaci (Supplementary) tare da neman buƙatar tsawonta janye tallafi man fetur zuwa watan Satumba na wannan shekara, ƙarin watanni uku kacal daga tsarin shekaru aru-aru da ake bi can baya bisa kyakkyawar fahimta da ba zai haddasa wani ruɗani ba”.

Kamar yadda Tilde ya ce, “Biyo bayan miƙa rahoton kwamiti, Shugaban Ƙasa zai tirke masu ruwa da tsaki da za su gano tantibin adadin kiyaye da gwamnati za ta lamunta a matsayin tallafi da kuma adadin kuɗaɗe da ‘yan ƙasa za su sadaukar wanda yin hakan ba zai zama ala-ƙaƙai a gare su ba, wato dai ciki lafiya, baka lafiya.

Dokta Aliyu Tilde sai ya yi koken a rusa gungun hukumar gudanar lwa ta Kamfanin na NNPC ba tare da la’akari da son zuciya ba daga Shugaba Tinubu, a kuma canja su da wasu nagartattun mutane waɗanda za su daƙile duk wata kafa ta cin hanci da rashawa, da kuma tabbatar da cewa mugun mai tsoratar wa tallafin man fetur bai dawo ba.

“Kuma za a cimma wannan manufa ce kawai idan kai, ko wani daga cikin iyalanka bai nuna sha’awa ko buƙatar zama jami’i ma kamfanin man fetur na MNPC ba. Domin a baya munga yadda shugabanni sukan bayar wa ‘yan matansu ko ‘ya’yansu mata muqamin ministan man fetur ko mamba a hukumar gudanarwa na kamfanin NNPC”.

Tilde ya ƙara shaida wa Shugaba Tinubu cewa, “Ta ire-iren waɗannan halayyar ne suka narke cikin tandun gambizar tallafin man fetur. Gareka, kamfanin NNPC ya kasance haramtaccen ɗan itace. Kada zuciya ta riya maka cin wannan ɗan itaciya, domin yin hakan babban zunubi ne gare ka.

“Kai ne magana, don haka wajibi ne ka ƙaddamar da bincike a cikin kamfanin NNPC. Ka ƙwato waɗannan ganima, tare da ɗaure waɗannan mugayen mutane. Ba damuwa ta ba ce idan ka wulaƙantasu irin yadda Yarima Muhammad bin Salman ya yi wa waɗansu sarakunan ƙasar Saudiyya, ya ɗaure su, tare da qwace ganimomi da suka wawashe. Kai ne namu. Bin Salman ɗin.

“Waɗannan magabata su ne mugaye masu laifuka. Ka fatattaki su tare da ƙwato ganimar da suka wawashe, kuma ka gamsu da tabbacin waɗannan mazambata sune mugaye masu laifuka. Ka fatattaki su tare da ƙwato ganimar da suka wawashe, kuma ka gamsu da tabbacin goyon bayan ‘yan Najeriya. Idan ka guji yin hakan, a sannu zaka vatadasu kuma ka yaƙe su. Kada koda wasa ka yarda a ruwa ka ta yadda zaka yi faɗa da talakawan ka, ko mambobin ƙungiyar ƙwadago, ka tunkari waɗancan mazambata”.

Tilde ya kuma yi kira da a sake duba dokar da ta kafa kamfanin NNPC da zummar yi masa gyara ta yadda kamfanin zai inganta amfaninsa wa ‘yan Nijeriya, yana mai cewar, tun wanzar da dokar kafa kamfanin, NNPC ta kasance saniya mai tsarkin tasa, maras lasafta komai. Takan kuma ayyana fibar ta bisa son zuciya, ta zuba adadin kuɗaɗen shigowa dabta kimanta cikin lalitar tarayyar Nijeriya da halin ko oho.

“Mu ‘yan Nijeriya ba mu bukatar wannan dodanniya. Wajibi ne gwamnati ta ƙa’idar da gudanar da kamfanin NNPC, la’akari da cewa man fetur ne babban kafar shigowar kiyaye wa gwamnati.

“Kamfanin NNPC yana fama da matsanancin cutar daji. Almundahana, cin hanci da rashawa sun mayar da kamfanin maras yin tagomashi cikin shekaru talatin da suka shuɗe. Kamfanin baya iya ko tatar gurvataccen mai, balle gyaran matatun man fetur, ko gina wasu sabbin, lamarin da Dangote shi kaɗai ya yi aikin ƙalilan shekaru, abinda kuma ƙasashe masu safarar mai suke yi cikin sauƙi. Abin takaici mu ne ƙasa ɗaya ƙwal daga cikin qasashe masu arzikin man fetur da muke sayen tataccen man fetur. Haƙiƙa, lokaci yazo da ƙasar dake ƙarƙashin jagorancin Magana da za a magance wa kamfanin wannan ƙeta da cutarwa.

Dokta Aliyu Tilde ya bayyana cewa matuƙar waɗannan shawarwari nasa suka samu karɓuwa, yana da yaƙinin ‘yan Nijeriya za su ke sayen man fetur akan farashin lita ɗaya Naira ɗari uku, yana mai cewar, yin hakan zai sanya gwamnati ta ɗauki nauyin wani tallafi, kazalika a share duk wata alamar ta da tsalle-tsallen cutarwa, kamar yadda yake a wasu ƙasashe masu arzikin man fetur.

Tilde ya bayar da tabbacin babu wani abinda zai rage wa shugaban ƙasa kimar sa ko daƙushe ikonsa, maimakon ma haka, amincewa da shawarwarin zai sanya ‘yan Nijeriya su jinjina masa a matsayin shugaba mai tunani ko karɓan shawarwari, mai tawali’u, maras tsoro, mai hikima, kuma mai damuwa da ‘yan ƙasarsa.