Gwamnan Neja ya rushe ofishin ’yan sandan da aka gina kan bututun ruwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Umaru Bago, ya rusa ofishin ’yan sanda na Chanchaga da ke Minna, Babban Birnin Jihar ta Neja.

A cewar wata sanarwa da mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa na zamani, Abdullberqy Ebbo, ya fitar, ta ce, an gina ofishin ’yan sandan ba bisa ƙa’ida ba a kan wani babban bututun ruwa.

Idan dai za a iya tunawa, gwamnan a yayin jawabinsa na ƙaddamar da ayyuka, ya sha alwashin rusa ofishin ’yan sandan, saboda kawo cikas ga samar da ruwan sha a babban birnin jihar.

Ebbo ya ce, ofishin ’yan sandan da ke kusa da hukumar ruwa ta jihar, an gina shi ne ba bisa ƙa’ida ba, saboda rashin mutunta ƙa’idojin tsare-tsaren gini.

“Ginin ba shi da izinin da ake buƙata kuma yana zaune a kan babban bututun ruwa. Gwamna Mohammed Umaru Bago, wanda ya sanya samar da ruwan sha a matsayin wani ɓangare na ajandarsa, zai yi duk abin da zai iya yi a matsayinsa na gwamna wajen samar da ruwan sha ga al’ummarsa,” inji sanarwar.

A halin da ake ciki, gwamnati ta kuma gargaɗi ƙungiyoyi, cibiyoyi, da ɗaiɗaikun jama’a da su nemi izini daga hukumomin da abin ya shafa kafin kafa wani gini.

Ya ƙara da cewa, gwamnati ba za ta yi qasa a gwiwa ba wajen ɗaukar ƙwararan matakai kan duk wanda aka samu yana son rashin bin doka da oda a jihar.

Hakazalika, gwamnan ya kuma bayar da umarnin soke takardar shaidar zama mai suna ‘C of O’, tare da rushe wani gidan mai na Ashrab Energy Limited nan take.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya ziyarci gidan mai da ke Ƙetaren Gwari, Minna.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar ta ce tsarin ya sabawa doka kuma yana barazana ga rayuwar al’ummar yankin.

Ya kuma ce mahukuntan gidan man sun yi watsi da umarnin da ya ba su na dakatar da aikin da ake yi.

“Mun samu rahoton tsarin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, kuma na nemi hukumar raya birane da ta dakatar da su daga aiki amma sun ci gaba, don haka mun soke takardar ‘C of O’ daga ranar, kuma za mu sanya masa alama don rushewa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *