Tsare Emefiele: DSS ta yi amai ta lashe

Hukumar tsaro ta DSS ta bayyana cewa, dakataccen Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, yana hannunta.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Peter Afunanya, shi ne ya sanar da haka a ranar Asabar.

Sanarwar da jami’in ya fitar ta ce, “DSS ta tabbatar da Mr Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), yanzu yana hannunta.”

Sanarwar ta kuma buƙaci jama’a, musamman ‘yan jarida da su lura da yadda suke ba da rahoto.

Da fari DSS ta ƙaryata rahoton da aka yaɗa cewa hukumar ta tsare Emefiele sa’a guda bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *