Nijeriya za ta ci gaba idan aka zuba jari mai yawa wajen ilimin ‘ya’ya mata – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bayyana cewa Nijeriya za ta iya samun gagarumin ci gaba idan aka zuba jari mai yawa a Shugaban Hukumar Ƙidaya na Ƙasa, Hon. Nasir Isa Kwarra, shi ne ya bayyana haka a yayin da hukumar ta shirya wani taron gabatar da rahoton yawan jama’a na ƙasa kamar yadda ta saba yi a duk shekara, a Birnin Tarayya Abuja.

A jawabinsa da farko, Hon. Kwarra ya nuna matuƙar farin cikinsa tare da yi wa baƙin da suka halarci taron maraba, inda ya bayyana cewa taron ya tattara su ne don ƙarin haske game da nasara da kuma ƙalubale na yawan jama’a da ake fuskanta a Nijeriya.

Kwarra ya bayyana cewa Rahoton Yanayin Yawan Jama’a na Duniya (SWOP) a kowace shekara ana fitar da shi, wanda a cewarsa babbar nasara ce ta Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA).

Wanda yawancin lokaci yana zuwa tare da jigon da ke haskaka yawan jama’a ko masu tasowa da matsalolin ci gaba tare da mayar da hankali ga ƙungiyoyin jama’a musamman mata, matasa, da ƙananan yara.

Taken taron na wannan shekara yana tunatar da jama’a ne game da nasarar da aka samu a duniya a ranar 15 ga Nuwamba, 2022, lokacin da duniya take da kimanin mutane biliyan 8.

Taken taron shi ne: “Rayuwar Jama’a Bilyan 8, Yiwuwa Mara Adadi: Ƙalubalen ‘Yanci da Zavuvvuka”. Ka ba ni dama in tunatar da cewa, Nijeriya na cikin kasashe takwas (Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Nijeriya, Pakistan, Philippines da Jamhuriyar Tanzaniya), waɗanda suka ba da gudummawar biliyan 8 da kuma inda fiye da rabin adadin ƙaruwar al’ummar duniya za a taru har zuwa shekarar 2050 kuma ana sa ran qasashe da ke Kudu da hamadar Sahara za su ba da gudummawar fiye da rabin qaruwar da ake sa ran zuwa shekarar 2050.

Shugaban ya cigaba da cewa, idan aka yi la’akari da ƙaruwar yawan al’umma a halin yanzu da kuma hasashen da ake yi a Nijeriya, Nijeriya za ta iya samun ci gaba idan aka sanya jari mai yawa da kuma niyya wajen samar da ingantaccen ilimi wanda zai dace da yanayin ’yan ƙwadago ta duniya wanda kuma zai amfanar da ‘ya’ya mata (muna buqatar mu sanya ‘yan matanmu a makaranta da kare su daga auren wuri ko na dole).

Ya ce ya kamata Nijeriya ta ƙara zuba jari don samar da isasshiyar kula da lafiya mai inganci da suka haɗa da tsarin iyali, qarfafa tsarin kiwon lafiya a matakin al’umma; samar da ingantattun ayyukan yi ga matasa; inganta ko ƙarfafa wa mata da tabbatar da tsaro tsaro.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: Kwamishinonin tarayya na NPC, Sakatarorin Dindindin, Daraktocin Cigaban Mata na Qasa, wakilin UNFPA, ma’aikatan diflomasiya/mambobin diflomasiyya, wakilin matasa, mambobin ƙungiyoyin jama’a, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *