16
Mar
Daga BASHIR ISAH Yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi ya kawo jiki, Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin taƙaita zirga-zirgar abubuwan hawa a kan tudu da ruwa da dangoginsu a ranar zaɓe. Wannan umarni zai fara aiki ne daga ƙarfe 12 na tsakar dare zuwa 6 na yamma na ranar zaɓen. Sai dai umarnin ya sahale wa jami'an INEC da masu sanya ido da 'yan jaridar da aka tantance da makamantansu damar zirga-zirga a wannan rana ta zaɓen. "Wannan umarni bai shafi yankin Abuja ba sakamakon babu wani zaɓe da za a gudanar…
