Labarai

Sufeto-Janar ya tura CP Usaini Gumel zuwa Kano a matsayin Kwamishinan’Yan Sandan jihar

Sufeto-Janar ya tura CP Usaini Gumel zuwa Kano a matsayin Kwamishinan’Yan Sandan jihar

Daga WAKILINMU Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali, ya sake soke tura wani Kwamishinan 'Yan Sanda zuwa Jihar Kano. IGP Alkali ya soke tura Feleye Olaleye a matsayin Kwamishinan 'Yan Sanda a Kano, kana ya maye gurbinsa da CP Ahmed Kontagora. Sai dai kuma, a wata sigina ta daban da rundunar ta ƙasa ta aike ta nuna yanzu IGP Alkali ya tura CP Usaini Gumel a matsayin Kwamishinan da zai jagoranci rundunar a Kano yayin zaɓen gwamnoni da ke tafe a jihar. A ranar 8 ga Maris IGP ya soke tura CP Balarabe Sule a matsayin wanda zai maye…
Read More
Tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka aka damƙe ɗan majalisar Bauchi, Yakubu Shehu – ‘Yan Sanda

Tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka aka damƙe ɗan majalisar Bauchi, Yakubu Shehu – ‘Yan Sanda

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce za ta ba da tukwicin kuɗi Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka mata wajen damƙe ɗan majalisa mai wakiltar Bauchi a Majalisar Wakilai, Yakubu Shehu, wanda take nema ruwa a jallo. Wannan na ƙunshe ne cikin jaridar 'yan sanda ta musamman mai lambar bugu - CB: 2685/Bsx/VOL.T/4s wadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya raba ranar Talata a Bauchi. Jaridar ta ce Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya, ƙarƙashin ikon Sufeto-Janar, Usman Baba, ta ayyana ɗan majalisa Yakubu Abdullahi Shehu a matsayin abin…
Read More
Bincike: Babu abin da za ku nema ku rasa, cewar INEC ga jam’iyyar LP

Bincike: Babu abin da za ku nema ku rasa, cewar INEC ga jam’iyyar LP

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce a shirye take ta ba da damar bincikar bayanan zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu ga duk jam'iyyar da ke da buƙatar hakan. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar lauyoyin Jam'iyyar Labour ƙarƙashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu, SAN, ranar Litinin a Abuja. Da yake jawabi, Yakubu ya faɗa wa lauyoyin cewa ya samu sanarwar zuwansu ta wasiƙar da aka aiko masa mai ɗauke da kwanan wata 6 ga Maris, don bincikar kayayyakin da aka yi amfani da su…
Read More
Ƙarancin kuɗi: Buhari bai hana Malami da Emefiele bin umarnin kotu ba, cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Ƙarancin kuɗi: Buhari bai hana Malami da Emefiele bin umarnin kotu ba, cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu inda Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗa wa Babban Lauyan Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele cewa su bijire wa umarnin Kotun Ƙoli game da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N1000, N500 da N200 zuwa Disamban bana ba. Babban kakakin Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja. Ya ce Shugaba Buhari bai umarci Malami da Emefiele su ƙi yin biyayya ga umarnin na kotu ba. Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar ta ce:…
Read More
Kotu ta ɗaure Odita Janar shekara 5 a Yobe

Kotu ta ɗaure Odita Janar shekara 5 a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu Alƙalin Babbar Kotun Jihar Yobe, Mai Shari'a Muhammad Lawu Lawan, ya garƙame Odita Janar na Ma'aikatar Ƙananan Hukumomin Jihar Yobe, Alhaji Idris Yahaya, a gidan yari na tsawon shekara biyar, sakamakon samunsa da aikata almundahana da kuɗaɗen al'umma, ranar Litinin. Kotun ta samu wanda ake zargin da laifin karkata akalar wasu kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 19,900,000 ba bisa ƙa'ida ba, wanda ofishin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na yankin, wanda yake a Maiduguri babban jihar Borno, ya gurfanar da shi. Bayanai sun nuna Alh. Yahaya ya karɓi wannan kuɗin…
Read More
Shugaban APC ya amince akwai aibi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar

Shugaban APC ya amince akwai aibi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Litinin ya ce, zaɓen shugaban ƙasa da ’yan majalisun tarayya wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 ba cikakken mara naƙasu bane, domin an samu aibi. Adamu ya faɗi haka ne a yayin da yake jawabi a wurin taron kwamitin gudanarwa na APC da shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima da zaɓaɓɓun mambobin majalisar tarayya. Taron na sirri wanda bai fara gudana ba sai da misalin ƙarfe 2:48 na rana a ɗakin taro na Banquet House da ke Abuja. Daga…
Read More
An sace ɗan takarar majalisar jiha kwana 4 kafin zaɓe a Ribas

An sace ɗan takarar majalisar jiha kwana 4 kafin zaɓe a Ribas

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Ribas sun sace ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar yayin da ya rage kwana huɗu kafin zaɓe. Chukwudi Ogbonna na takarar Majalisar Dokokin jihar ne ƙarƙashin Jam'iyyar Accord, inda yake neman wakilcin al'ummar yankunan Ogba/Egbema/Ndoni da ke jihar. Bayanai daga yankin sun ce an sace Ogbonna ne ranar Litinin a motarsa a lokacin da yake tuƙi a yankin Rumuigbo da ke kusa da Fatakwal, inda 'yan bindigar suka tsare shi kana suka yi awon gaba da shi. Wani ɗan uwan ɗan takarar mai suna Ifeaka Nwakiri, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga…
Read More
Soja ya harbe abokin aikinsa sannan ya kashe kansa

Soja ya harbe abokin aikinsa sannan ya kashe kansa

Rundunar Sojin Nijeriya ta fara bincike kan wani soja kan zargin harbe abokan aikinsa har lahira sannan ya kashe kansa a sansanin sojoji da ke Rabbah a Jihar Sakkwato. Kakakin rundunar, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a tantance haqiqanin abin da ya faru ba, amma dai sojan ya harbe kansa bayan hallaka abokin aikin nasa. Nwachukwu ya kara da cewa Babban Hafsan Runduna ta 8 (GOC) kuma Kwamandan hundunar haɗin gwiwa ta Operation Northwest, Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut, da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wajen da lamarin ya afku. A cewarsa, GOC ya…
Read More
Mutanen da suka fi taka rawar gani wajen samun ’yancin Nijeriya

Mutanen da suka fi taka rawar gani wajen samun ’yancin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jaridar Blueprint Manahaja ta yi bincike daga wurare daban-daban dangane da mutanen da suka fi taka rawa wajen fafutukar nema wa Nijeriya ’yanci. Za mu tattaro mutum bakwai waɗanda suka yi fice wajen samun ’yancin: Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto (Yuni 12, 1910 - Janairu 15, 1966): An haifi Sir Ahmadu Bello a garin Rabbah na jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya. Sardauna na daya daga cikin jagororin Nijeriya da suka yi fice a duniya. Ahmadu Bello ya riqe sarautar Sardaunan Sokoto kuma ya jagoranci jam'iyyar Northern People's Congress (NPC), inda ya mamaye harkar siyasar kasar…
Read More
An sake tura sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda a Kano

An sake tura sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Babban Sufeton 'Yan Sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya turs CP Ahmad Kontagora, zuwa Kano a matsayin sabon Kwamishinan 'Yan Sanda da zai jagoranci gudanar da zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokoki na jihar. Wannan ya biyo bayan dakatar da turo CP Feleye Olaleye da Babban Sufeton 'Yan Sandan ya yi, bayan an turo shi a makon da ya gabata a matsayin Kwamishinan 'Yan Sandan Kano. A 'yan kwanakin nan dai rundunar 'yan sandan ta turo kwamishinonin 'yan sanda akai-akai zuwa Jihar Kano, wanda ya janyo ƙorafi da gudanar da zanga-zanga daga magoya bayan…
Read More