Labarai

Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnati kwana 7 ta kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗi

Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnati kwana 7 ta kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana bakwai ta kawo ƙarshen wahalar man fetur da ta takardun kuɗi a faɗin ƙasar nan. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero, ne ya sanar da lokacin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar ƙungiyar ta ƙasa da ke Abuja, kan matsayin taron ƙungiyar ranar Litinin. Ya ce, matuƙar ba a iya magance matsalolin ba nan da cikar wa’adin, za su tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar wanda ya koka da irin mawuyacin halin da wahalhalun suka jefa ’yan Nijeriya, musamman ma ma’aikata ya sa ƙungiyar…
Read More
Gobara ta tashi a Kasuwar Singa dake Kano

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa dake Kano

Daga WAKILINMU Bayanai daga Kano sun tabbatar da aukuwar gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Kano, wato Kasuwar Singa. Majiyarmu ta ce gobarar ta fara ne da tsakar daren da ya gabata zuwa safiyar Litinin. An ga jami'an kwana-kwana tare da 'yan kasuwar a lokacin da suke ƙoƙarin kashe gobarar wadda ta ƙone shaguna da daman gaske. Abubakar Aminu, na ɗaya daga cikin 'yan kasuwar da gobarar ta shafa, ya shaida wa jaridar News Point cewa ya samu kiran waya da misalin ƙarfe 1:15 na dare, kuma da ya isa kasuwar da misalin ƙarfe 2:00 na daren, ya tarar da…
Read More
Canjin kuɗi: Gwamnoni sun bai wa Malami, Emiefele wa’adin biyayya ga umarnin kotu

Canjin kuɗi: Gwamnoni sun bai wa Malami, Emiefele wa’adin biyayya ga umarnin kotu

Daga BASHIR ISAH Gwamnonin da suka maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan batun canjin kuɗi sun bai wa Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, tare da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, zuwa ranar Talata kan su yi wa umarnin Kotun Ƙoli biyayya. Gwamnonin na buƙatar Gwamnati da CBN su mutunta umarnin kotu wajen tsawaita wa'adin tsoffin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000 zuwa 31 ga Disamban 2023 kamar yadda kotun ta buƙata. Gwamnonin sun yi barazanar shigar da ƙara kotu a kan Malami da Emefiele muddin aka wuce ranar Talata ba tare da sun…
Read More
Kar a zargi Gwamna Buni wajen faɗuwar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa a Yobe – Injiniya Umar Ali

Kar a zargi Gwamna Buni wajen faɗuwar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa a Yobe – Injiniya Umar Ali

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu An bayyana cewa rashin wakilci nagari, ta fuskar 'yan majalisar dokokin Yobe, shugabanin ƙananan hukumomi, tare da wakilan al'umma a matakai daban-daban a matsayin tarnaƙin da ya dabaibaye jam'iyyar APC ta sha mummunan kaye, a zaɓen Shugaban Ƙasa haɗe da na 'yan majalisun a makonnin da suka gabata a jihar Yobe. Wannan furucin ya fito ne daga bakin ɗan takarar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam'iyyar APC da NNPP a zaɓukan fidda-gwani na shekarar 2019 da 2022, Engr. Malam Umar Ali, wanda halin yanzu na hannun daman Gwamnan jihar Yobe ne, Mai Mala Buni, a…
Read More
CBN ya kammala shirin canjin kuɗi a yankunan karkara

CBN ya kammala shirin canjin kuɗi a yankunan karkara

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ce ya kammala shirin canjin tsoffin kuɗi da sabo a yankunan karkara da sauran yankunan da babu bankuna. Muƙaddashin Kakakin CBN, Isa Abdulmumin, ne ya bayyana haka tare da cewa shirin ya cimma manufarsa. A cewarsa, “Shirin ya kammala. Shirin abu ne mai ƙayyadadden lokaci amma ba wanda zai ci gaba da gudana ba." Sai dai Ƙungiyar Masu Hada-hadar Kuɗi ta Waya da Wakilan Bankuna a Nijeriya, ta bayyana shirin a matsayin mara armashi, saboda taƙaita damawa da masu ruwa da tsaki a cikinsa. CBN ya ce an samar da shirin ne…
Read More
Ɓata-gari sun cinna wa ɓangaren ƙabilar Ibo a kasuwar Legas wuta

Ɓata-gari sun cinna wa ɓangaren ƙabilar Ibo a kasuwar Legas wuta

Daga AMINA YUSUF ALI Ana zargin wasu ɓata-gari da cinna wuta wacce har ta yi sanadiyyar tayar da gobara a kasuwar Legas ta sayar da kayayyakin gyaran mota wacce mafi akasarin ahalinta inyamurai ne, wato 'yan ƙabilar Ibo. Wannan kasuwar sayar da kayan gyaran mota tana kan titin Kirikiri, Ajegunle, ƙaramar hukumar Ajeromi ifelodun ta jihar Legas. Al'amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, 8 ga Maris, 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hari da aka kai kasuwar sayar da kayan mota wacce akasarinta ƙabilar Ibo ne suke da rinjaye a cikinta an yi shi ne da gayya kuma…
Read More
NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jam'iyyar NNPP a Jihar Katsina ta kori wasu jiga-jigan jam'iyyar ciki har da mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar, Muttaqa Rabe Darma da shugaban jam'iyyar, Alhaji Sani Liti da sakatarenta Alhaji Mustapha Bashir da kuma shugaban matasa da shugabannin jam'iyyar na shiyyoyin Katsina, Daura da kuma Funtua. Kakakin jam'iyyar, Alhaji Nasiru Usman Kankia ne ya bayyana wa manema labarai hakan lokacin da yake ƙarin bayani dangane da lamarin a Katsina. A cewar kakakin, an kori mutanen ne bisa aikata laifin yi wa jam'iyya zagon ƙasa. Ya ƙara da cewa shugabannin jam'iyyar sun kira wani taron da…
Read More
Direban motar da jirgin ƙasa ya yi awon gaba da ita a Legas, ya nemi afuwa

Direban motar da jirgin ƙasa ya yi awon gaba da ita a Legas, ya nemi afuwa

Daga BASHIR ISAH Direban bas ɗin da ta yi hatsari da jirgin ƙasa ran Alhamis da ta gabata a Legas, Oluwaseun Osinbajo, ya nemi afuwar waɗanda hatsarin ya rutsa da su a cikin motar. Direban ya yi zargin matsalar da motar ke fama da ita a wannan lokaci ya sa hakan ta faru. Tuni dai aka tura direban, wanda ma'aikaci ne a Ma'aikatar Sufuri ta Jihar Legas, Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar don gudanar da bincike kan aukuwar hatsarin. Motar da lamarin ya shafa ta yi taho-mu-gama da jirgin ƙasan ne ɗauke da ma'aikatan da ke ƙoƙarin zuwa wajen…
Read More
Akwai alaƙa mai kyau tsakanina da gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashinsu  – Gawuna

Akwai alaƙa mai kyau tsakanina da gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashinsu – Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewar akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da dukkanin gwamnonin da ya yi aiki ƙarƙashinsu a jihar. Gawuna ya bayyana hakan ne a gidan Talabijin na TVC a cikin shirin “Countdown Nigeria Decides 2023” da aka yi tare da shi. A cewarsa, “Ina da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran tsofaffin gwamnonin da na yi aiki da su a gwamnatocin baya a matsayin shugaban ƙaramar hukuma, kwamishina da kuma a yanzu a matsayina na Mataimakin…
Read More
Hukumar tsaro ta damƙe mutum 4 da jabun sabon kuɗi na N1.9m

Hukumar tsaro ta damƙe mutum 4 da jabun sabon kuɗi na N1.9m

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta kama wasu mutum huɗu da suka ƙware wajen buga jabun kuɗaɗe. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, Kakakin NSCDC, Kwamanda Olusola Odumosu, ya ce an damƙe waɗanda lamarin ya shafa ne a garin Jos, babban birnin Jihar Filato. A cewar Odumosu sun kama tawagar farko da ta ƙunshi mutum huɗu da jabun kuɗi Dala 64,800 fa kuma Naira 475,000. Yayin da suka kama tawaga ta biyu mai ƙunshe da mutum biyar ɗauke da jabun Naira miliyan 1.5. Ya ce duka waɗanda aka kama ɗin 'yan shekara tsakanin 24 zuwa 56.
Read More