Labarai

APC za ta gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisunta kan shugabancin Majalisar Tarayya

APC za ta gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisunta kan shugabancin Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC za ta gana da zaɓaɓɓun sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai ya zuwa ranar Litinin mai zuwa domin tattauna batun shugabancin Majalisa karo na 10 da ake shirin kafawa. Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar ns Ƙasa ne zai gana da 'yan majalisun inda ake sa ran samar da tsare-tsaren da za su taimaka wa 'yan jam'iyyar samun muƙamai a shugabancin majalisun. Sanarwar taron wadda aka fitar ranar Juma'a da daddare, mai taken "Gayyata zuwa ga ɗaukacin zaɓaɓɓun sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai”, Sakataren jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ne ya rattaba mata hannu. “Ana sanar da…
Read More
Shugaban INEC ya yi barazanar maka PDP a kotu kan zargin ɓata masa suna

Shugaban INEC ya yi barazanar maka PDP a kotu kan zargin ɓata masa suna

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Mahmood Yakubu, ya shawarci jami'an Jam'iyyar PDP da su guji aibata shi a kafafen yaɗa labarai ko kuma su ya ɗauki matakin shari'a. Babban Sakataren Yaɗa Labaran Shugaban na INEC, Mr Rotimi Oyekanmi, shi ne ya bayyana haka a matsayin raddi ga kiran da PDP ta yi na sai dai Farfesa Yakubu ya sauka daga muƙaminsa. PDP ta buƙaci Yakubu ya sauka daga muƙaminsa a matsayinsa na mai gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisar Tarayya, saboda zargin tafka maguɗi. Lamarin da Yakubu ya ce idan akwai abin da PDP ba…
Read More
Wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin ƙaddamar da Majalisar Dokokin Ƙasar karo na 10 a watan Yuni, wasu zaɓaɓɓun sanatoci sun fara fafutukar neman shugabancin majalisar. Ana sa ran masu neman kujerun majalisar dattawa da ta wakilai za su fara bayyana sha’awarsu a kan muƙaman da suka zaɓa da zarar majalisar dokokin ƙasar ta dawo daga hutun zace a ranar 20 ga watan Maris. Baya ga shugabancin majalisar dattawa, sauran muqaman da za a naɗa sun haɗa da kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa da kuma manyan muƙamai. Bisa al'adar majalisa, manyan mambobi - 'yan majalisa masu wa'adi biyu…
Read More
Gwamnan Kogi ya yi barazanar kama masu ƙin karɓar tsoffin kuɗi a jiharsa

Gwamnan Kogi ya yi barazanar kama masu ƙin karɓar tsoffin kuɗi a jiharsa

Daga BASHIR ISAH Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya yi barazanar kamawa da hukunta masu ƙin karɓar tsoffin kuɗi a jiharsa. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Labarai da Sadarwa na Jihar, Mr Kingsley Fanwo, ya fitar a Lakwaja babban birnin jihar. A ranar Larabar da ta gabata Koton Ƙoli ta yanke hukuncin ci gaba da a,mfani da tsoffin takardun kuɗi na N1000, N500 da N200 har zuwa Disamban 2023. Da wannan Gwamnan Yahaya ya ce ba daidai ba ne ƙin karvar tsoffin kuɗin duk da Kotun Ƙoli ta ba da damar haka. “Wannan gwamnatin ba za…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta ɗage Shirin Ƙidayar Al’umma zuwa Mayu

Gwamnatin Tarayya za ta ɗage Shirin Ƙidayar Al’umma zuwa Mayu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Q'Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), ta ce ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da aka yi zai shafi Aikin Ƙidayar Jama'a na 2023. Idan za a iya tunawa, NPC ta shirya gudanar da aikin ƙidayar daga ranar 29 ga Maris zuwa Afrilu bayan shafe shekaru 17. Wata majiya daga hukumar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce har yanzu dai hukumar ba ta yi matsaya ba amma ana kyautata zaton yanzu aikin ƙidayar zai gudana ne tsakanin 3 zuwa 7 ga watan Mayu mai zuwa. “Shirin ƙidayar zai gudana ne daga 3 zuwa 7…
Read More
Dalilina na ƙin karɓar takardar shaidar cin zaɓe a NNPP – Sanata Shekarau

Dalilina na ƙin karɓar takardar shaidar cin zaɓe a NNPP – Sanata Shekarau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilinsa na ƙaurace wa taron miƙa wa  zaɓaɓɓun sanatoci takardar shaidar lashe zaɓen da aka gudanar a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, a makon nan. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Malam Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a ƙarƙashin jtsohuwar jam’iyyarsa ta NNPP maimakon jam’iyyarsa ta yanzu, PDP. Sai dai ɗan majalisar mai ci bai halarci taron miqa takardar shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun sanatocin ba a ranar Talatar da ta gabata.…
Read More
Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani yanayi mai nuna alamun kutingwila ga lashe zaɓen 2023 da zavavven Shugaban Ƙasa mai jiran gado a Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi, wasu ’yan Nijeriya da dama mazauna Birnin Landon, Babban Birnin Ƙasar Ingila, sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar dake birnin Landan ɗin na ƙasar Birtaniya. Wannan ya faru ne jim kaɗan bayan Chatham House ya soki lamarin yadda aka tattara sakamakon zaɓen, wanda ya bai wa Tinubun nasara, inda gidan na dimukraɗiyya ya ce, ba a bi qa’idojin zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman…
Read More
Zannan Kwankwasiyya ya raba tallafin injinan bada wuta ga makarantun islamiyya a Jihar Kano

Zannan Kwankwasiyya ya raba tallafin injinan bada wuta ga makarantun islamiyya a Jihar Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jigo a tafiyar Kwankwasiyya a qaramar hukumar Nasarawa, Alhaji Abubakar Yahuza Gama, Zannan Kwankwasiyya ya tallafa wa wata ɗaliba Fatima Aminu da ta yi nasarar zama ta ɗaya a musabaƙar karatun Ƙur'ani da kayan ɗaki tare da bai wa makarantun Islamiyya 48 injinan bada wutar lantarki don haskaka makarantun, ƙarƙashin ƙungiyar haɗin kan makarantun Islamiyya. A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na Mento a ranar Alhamis, Zannan na Kwankwasiyya ya kuma bada kyautar firji guda biyar ga ɗaliban makarantun Islamiyya da suka yi nasara a musabaƙa na Sira da sauran fannoni na…
Read More
Ranar Mata: Ƙungiya ta horar da mata 100 girki a Kano

Ranar Mata: Ƙungiya ta horar da mata 100 girki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Northern Chef Kamal Foundation ta horar da mata guda 100 dabarub girke-girke daban-daban, saboda ƙaratowar azumi, da ya  gudana a ranar Laraba a Unguwar Hotoro dake Kano, inda taron ya zo daidai da Ranar Mata ta Duniya. Da yake jawabi a wajen, shugaban ƙungiyar kuma wanda ya ƙirƙiri ƙungiyar Chef Kamal Ahmad ya ce ƙungiyar ta shirya taron ne domin horar da mata 100 da kuma murnar zagayowar ranar mata ta duniya. Ya ce babban maƙasudin horarswar shi ne samar da ingantaccen abinci mai gina jiki musamman a wannan wata na azumin Ramadan da…
Read More
Mutane da dama sun rasu a taho-mu-gamar motar bas da ta siminti

Mutane da dama sun rasu a taho-mu-gamar motar bas da ta siminti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla mutane 10 ne ake fargabar sun mutu sakamakon wani karo da wata motar bas ta kasuwanci da wata babbar mota maƙare da siminti a hanyar Inugu zuwa Onitsha. Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 9 na safe kusa da tashar motar CBN dake Inugu a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris, 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, motar bas mai ɗauke da mutane 18 mai lamba Enugu XL884 ENU ta shiga cikin wata tirela mai shigowa ɗauke da buhunan siminti. Motocin biyu suna tafiya ne a kan hanya ɗaya sakamakon munanan ramika da…
Read More