Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Aƙalla mutane 10 ne ake fargabar sun mutu sakamakon wani karo da wata motar bas ta kasuwanci da wata babbar mota maƙare da siminti a hanyar Inugu zuwa Onitsha.
Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 9 na safe kusa da tashar motar CBN dake Inugu a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris, 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa, motar bas mai ɗauke da mutane 18 mai lamba Enugu XL884 ENU ta shiga cikin wata tirela mai shigowa ɗauke da buhunan siminti.
Motocin biyu suna tafiya ne a kan hanya ɗaya sakamakon munanan ramika da aka samu a ɗaya hannun.
An tattaro cewa jami’an kiyaye haɗurra da suka yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru sun ciro aƙalla gawarwaki bakwai daga cikin tarkacen motocin.
An garzaya da wasu fasinjojin da suka suma zuwa wani asibiti da ke kusa, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwar wasu fasinjojin da suka isa asibitin.
Da dama dai sun danganta faruwar hatsarin da rashin kyawun hanyar wanda ya tilasta wa masu ababen hawa tafiya ta hanya ɗaya.
Tuni dai ‘yan sanda da sojoji da kuma jami’an kiyaye haɗɗura suka fito domin kula da ababen hawa da kuma kauce wa taɓarɓarewar doka.
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan wata mota ƙirar BRT ta yi karo da jirgin ƙasa a yankin PWD da yake Jihar Legas. Lamarin dai ya yi sanadiyyar rayuka biyu tare da jikkata wasu da dama.