Labarai

Ba mu umarci bankuna su bada tsofaffin takardun kuɗi ba – CBN

Ba mu umarci bankuna su bada tsofaffin takardun kuɗi ba – CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ranar Talata ya ce bai bayar da wani sabon umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata na bayar da umarnin a riqa rarraba tsofaffin takardun Naira tare da sabbi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba. Kwamitin alqalai na mutane bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, ya bayyana a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, akan umarnin da Shugaban Ƙasa ya bada. Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasar CBN na sake gyarawa…
Read More
DSS ta samar da kafafenta a soshiyal midiya

DSS ta samar da kafafenta a soshiyal midiya

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS, ta ce ta ƙirƙiro da shafukan sohiyal domin bunƙasa hanyoyinta na hulɗa da jama'a da masu ruwa da tsaki. Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukunar, Dr Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja. Ya ce shafukan da suka ƙirƙiro sun haɗa da:Twitter: @OfficialDSSNG Facebook: OfficialDSSNG Instagram: @OfficialDSSNG A cewarsa, shafin Tiwita na PRO na hukumar shi ne: @DrAfunanya_PNA. Ya ce kafin wannan lokaci hukumar ba ta da waɗanan kafafe, kuma tana sa ran soma amfani da su ne daga ranar 6 ga Maris. Jami'in ya ce al'umma su sani cewar,…
Read More
Mazauna Abuja na fuskantar matsanancin matsalar fetur

Mazauna Abuja na fuskantar matsanancin matsalar fetur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Yawancin masu ababen hawa a Babban Birnin Tarayya Abuja, na fuskantar matsalar man fetur da dogayen layuka ake cigaba da yi a gidajen man. Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya da ya sa ido a gidajen mai a Abuja a ranar Talata, ya ba da rahoton cewa, yawancin gidajen fetur ɗin a rufe suke, yayin da kaɗan ne kawai ke badawa, wanda ya haifar da mummunar cunkoson ababen hawa saboda dogayen layukan da ake yi. Masu motocin sun kuma nuna rashin jin daɗinsu kan ƙarancin tsabar kuɗaɗen da ake samu a ƙasar nan, wanda suka ce…
Read More
APC ta naɗa manyan lauyoyin da za su kare nasarar Tinubu a kotu

APC ta naɗa manyan lauyoyin da za su kare nasarar Tinubu a kotu

Daga WAKILINMU Jam’iyyar APC ta haɗa kan wasu manyan lauyoyi su 12 don su wakilce ta a kotu kan ƙarar da aka shigar kotu dangane da zaɓen Shugaban Ƙasar da ya gabata. Sanarwar da APC ta fitar ta hannun mai ba ta shawara kan sha’anin shari’a, Ahmad El-Marzuq, ta ce tawagar na ƙunshe da ƙwararrun lauyoyi da suka goge a fagen shari’a zaɓe. El-Marzuq ya ce lauyoyin za su gudanar da aikinsu ne ƙarƙashin jagorancin fitaccen lauyan nan masanin makamar aiki, wato Prince Lateef Fagbemi. Ya yi kira ga mambobin APC da su bai wa lauyoyin haɗin kan da ya…
Read More
Zargin maguɗi: INEC ta dakatar da Kwamishin Zaɓe na Sakkwato

Zargin maguɗi: INEC ta dakatar da Kwamishin Zaɓe na Sakkwato

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Sakkwato, Nura Ali, bisa zargin tafka maguɗi. Bayanin dakatarwar na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakatariyar INEC, Rose Orlaran-Anthony, wadda hukumar ta aike wa Kwamishinan da kuma Sakataren hukumar na Jihar Sakkwato. A cewar wasiƙar mai ɗauke da lamba: INEC/SCE/442/V.II, “Wannan shi ne don sanar da matsayar hukumar a kanka (Dr Nura Ali), Kwamishinan Zaɓe na Jihar Sakkwato, cewa ka yi nesa da ofishin hukumar a Jihar Sakkwato har sai abin da hali ya yi.” INEC ta ba da…
Read More
Amfani da tsohon kuɗi: Har yanzu bankuna a Abuja ba su bi umarnin Kotun Ƙoli ba

Amfani da tsohon kuɗi: Har yanzu bankuna a Abuja ba su bi umarnin Kotun Ƙoli ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Har yanzu ’yan Nijeriya ba su samu wadataccen sababbi da tsofaffin takardun Naira ba kwanaki bayan da Kotun Ƙoli ta bayar da umarni ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) kan cigana da amfani tsoffin takardar kuɗi daga ranar 10 ga watan Fabrairu. Har yanzu dai bankunan da ke Abuja ba su nuna gamsuwarsu kam wannan batu ba, saboda har yanzu mazauna garin na fuskantar matsalolin ƙarancin kuɗi a wuraren cire kuɗi na ATM na POS. A ranar Juma’a ne ƙotun ƙolin ƙasar ta halasta amfani da wasu tsofaffin takardun kuɗin Naira a matsayin takardar kuɗi har zuwa…
Read More
Ganduje ya yi wa fursunoni da dama afuwa

Ganduje ya yi wa fursunoni da dama afuwa

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ba da umarnin a saki wasu fursunoni 12 daga gidan yari a ranar Talata. Wannan na zuwa ne yayi da ya rage kwanaki ƙalilaln kafin zaɓe gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da za a gudanar a faɗin ƙasa. Bayanin afuwar na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin hukumar kula da gidan yari na Kano, SC Musbahu Lawan Ƙofar Nasarawa ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya yafe ma waɗanda aka yanke wa hukuncin kisan ne a ranar Talata, kuma ya umarci…
Read More
Dattijon ƙasa, Musan Musawa ya rasu yana da shekara 86

Dattijon ƙasa, Musan Musawa ya rasu yana da shekara 86

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa dattijon ƙasa, Alhaji Musan Musawa rasuwa yana da shekara 86. Marigayin ya rasu ne ranar Talata bayan fama da rashin lafiya. An haifi marigayin ne ran 1 ga Afrilun 1937, tsohon ɗan jarida, diflomasiyya, siyasa ne. Ya rasu ya bar 'ya'ya da dangi da dama, ciki har da mataimakiyar kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC, Barista Hannatu Musawa, wadda marubuciya ce a Jaridar Leadership. Tuni zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhini tare da miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin. Cikin sanarwar da ya…
Read More
Sunan Alhassan Doguwa ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen waɗanda suka ci zaɓe

Sunan Alhassan Doguwa ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen waɗanda suka ci zaɓe

Daga BASHIR ISAH Sunan Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakila, Alhassan Ado Doguwa, ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen 'yan majalisun da suka lashe zaɓe a zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana ranar 25 ga Fabrairu. Wannan na zuwa ne bayan da kotu ta amince ta ba da belin ɗan majalisar wanda ke tsare a kurkuku bisa zargin haddasa rikicin siyasa. Duk da dai an ayya Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen yankinsu, sai dai ba a ga sunansa ba daga jerin sunayen 'yan takarar da Hukumar INEC ta fitar a ranar Talata…
Read More
Ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba ya ƙin sakamakon zaɓe ko da an tafaka maguɗi – Tinubu

Ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba ya ƙin sakamakon zaɓe ko da an tafaka maguɗi – Tinubu

Daga WAKILINMU Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar ɗan dimokuraɗiyya na gaske ba zai ƙi karɓar sakamakon zaɓe ba ko da kuwa an tafka maguɗi a zaɓen. Tinubu ya faɗi haka ne a matsayin martani ga 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi. Tun ana tsaka da tattara ƙurin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, Atiku da Obi suka buƙaci a soke zaɓen. Sun bukaci hakan ne bayan da suka yi zargin an tafa maguɗi sakamakon rashin amfani da na'urar BVAS. Da yake amsa tambayar manema labarai bayan ziyarar…
Read More