Ba mu umarci bankuna su bada tsofaffin takardun kuɗi ba – CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ranar Talata ya ce bai bayar da wani sabon umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata na bayar da umarnin a riqa rarraba tsofaffin takardun Naira tare da sabbi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Kwamitin alqalai na mutane bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, ya bayyana a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, akan umarnin da Shugaban Ƙasa ya bada.

Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasar CBN na sake gyarawa tare da cire tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da N1,000, ba tare da tuntuɓar jihohi ba, Gwamnatin Tarayya. Majalisar Wakilai da sauran masu ruwa da tsaki.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samu ruɗani a tsakanin bankunan kasuwanci da ‘yan kasuwa biyo bayan rashin bayar da umarnin da Babban Bankin CBN ya bayar na karɓar tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000.

Kakakin Babban Bankin na CBN, Isa Abdulmumin, wanda ya zanta da wakilinmu, ya ce CBN ɗin bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Sai dai wani babban jami’in hukumar da ya zanta da Daily Trust ya ce: “Tsofaffi da kuma sababbin takardun kuɗi ne na doka, kuma a halin yanzu bankuna suna ba da su ga kwastomomi. Kada ‘yan Nijeriya su yi watsi da duk wata sanarwa, ko tsoho ko sabo.”

Ƙarin bankunan kasuwanci a faɗin ƙasar nan sun fara fitar da tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000 ga kwastomominsu.

Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Daily Trust ta ruwaito cewa Bankin Guarantee Trust Bank (GTB) ya fara raba tsofaffin takardun kuɗi a rassansa a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

Binciken da wakilinmu ya yi a Legas ya nuna cewa bankuna sun fara bayar da tsofaffin takardun kuɗi na Naira ga kwastomomi a rumbun ATM daban-daban da kuma kan kantuna.

Reshen bankin Zenith da ke garin Festac ya biya tsofaffin takardun kuɗi ga abokan ciniki. Haka kuma na’urorin ATM da ke rassan bankin UBA da ke kusa da gadar Agege-Pen Cinema, da GTB da ke unguwar Ikeja a Legas, su ma suna raba tsofaffin takardun kuɗi.

Binciken ya kuma nuna cewa bankin WEMA ya umurci rassansa da su fara raba tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000 a faɗin ƙasar.

Har ila yau, wani jami’in bankin Zenith wanda ya so a sakaya sunansa ya ce reshen “mun samu umarnin fara raba tsofaffin takardun kuɗi ga abokan cinikinmu.” Wani ma’aikacin bankin Zenith, Barista Dike Amadi ya ce, “An biya ni da tsoffin kudi Naira 500 a yammacin yau a wani reshen bankin Zenith da ke Fatakwal.”

Wani abokin ciniki mai suna Aina Dipo, ya ce, “yanzu ana bayar da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 500 da N1000 a Osogbo, Jihar Osun.”

FirstBank, Polaris da Unity ba su yanke shawara ba

Wani cak a bankin First Bank da Polaris da kuma bankin Unity, ya nuna cewa suna raba tsohuwar Naira 200 ne kawai kamar yadda Babban Bankin Ƙasar CBN ya umarta.

Wani manajan bankin First Bank da ke Kano ya ce: “Ba mu samu wani umarni daga bankin CBN na karɓar tsofaffin takardun kuɗi ba, shi ya sa hakan ba ya faruwa kamar yadda muke magana.”

Sai dai kuma an sake samun wani sabon salo a dambarwar, inda manyan kantuna da gidajen mai da direbobin bas na kasuwanci a wasu sassan Legas ke ƙin amincewa da tsofaffin takardun kuɗin.

Olaiya Simileoluwa, wani mazaunin Legas ya ce, “wane irin ruɗani ne wannan? Kotun Ƙoli ta ce a cigaba da amfani da tsoffin takardun kuɗin har zuwa watan Disamba, bankuna sun fara rarraba tsofaffin takardun kuɗi amma direbobin bas, manyan kantuna, gidajen mai, da sauransu ba sa karɓa. Kamar dai ƙasar nan ba ta daidaita ba.”

Hakazalika, Kate Hensley Haziel wadda ita ma da ke zaune a Legas ta ce, “Ina ganin bayan hukuncin Kotun Ƙoli, tsohuwar Naira 500 da 1000 za su ci gaba da zama a kan doka har zuwa Disamba 2023. Akwai buƙatar CBN ya yi wa ‘yan ƙasa bayani. Mutane da yawa har yanzu suna cikin ruɗani game da ko za su karɓi tsoffin kuɗin ko a’a. ”

Wani masani kan harkokin kuɗi, Gbolade Idakolo, ya ce ya kamata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gaggauta umurtar Gwamnan CBN ya dubi halin da ake ciki. “Manufar sake fasalin Naira ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa da sama da tiriliyan guda a asarar kasuwanci. Yawancin masu matsakaita da ƙananan sana’o’i sun rufe shaguna saboda mu’amalarsu da tsabar kuɗi kai tsaye.

“Manufar ta qara wahalhalu ga al’ummar da ke cikin damuwa, kuma hukuncin Kotun Ƙoli ya kasance wani babban taimako ga ‘yan ƙasar,” inji shi.