19
Aug
Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Matasan Jam'iyyar PDP sun gudanar da bikin ranar matasa ta duniya 12 ga Agustan 2022 a Abuja, yayin wani ƙayataccen taro da ya samu halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar daga sassan ƙasar nan ciki har da ɗan takarar shugabancin ƙasar nan na Jam'iyyar PDP a zaven baɗi Atiku Abubakar da Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa Dr. Iyorchia Ayu da sauran shugabanni. A jawabinsa na buɗe taron, shugaban matasa na Jam'iyyar ta PDP Prince Muhammad Kadaɗe Sulaiman ya ce manufar taron mai taken: 'Haɗin gwiwar gudanar da shugabanci tare da mtasa na cikin muradun cigaba mai ɗorewa na…
