21
Aug
Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya samu gagarumar tarba cikin ƙasaitaccen biki a garin Jada, wanda nan ne mahaifarsa. Da ya ke masa maraba, cikin ƙasaitaccen yanayi da aka shirya na musamman, shugaban ƙaramar hukumar Jada Honorable Salisu Muhammed Solo ya ce, suna mutuƙar alfahari da kasancewar Atiku ɗansu, inda ya yi alƙawarin mara masa baya a takarar shugabancin Nijeriya da ya ke yi. A jawabinsa yayin taron, Sanata Dino Melaye ya bayyana muhimmancin ziyayar zuwa gida, inda yace wannan ya nuna cewar Atiku ya san asalin sa…
