15
May
Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar sojojin Nijeriya ta biya dukkan haƙƙoƙin tsofaffin jami’anta da kuma na magadan sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Hukumar kula da fanshon sojoji (MPB) ta kammala biyan ƙarin mafi ƙarancin albashi da kuma basussukan albashi ga tsaffin ma'aikatan da suka cancanta, wanda aka fara tun ranar 6 ga Mayu, 2022, wanda aka kammala a ranar 10 ga Mayu, 2022. Hakazalika, hukumar ta iya dukkan iyalan mamatan sojojin waɗanda suke bin bashin haƙƙoƙinsu su ma an biya su, ba sa bin ko sisi. Don haka, hukumar fanshon sojojin ta cika alƙawuran da ta ɗaukar…
