Ban san yadda aka yi Hanifa ta mutu ba – Tanko

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da a ke zargi da kashe Hanifa Abubakar, ya ce shi da sauran mutane biyu da ake tuhuma ba su san yadda a ka yi yarinyar ‘yar shekara 5 da haihuwa ta rasu ba.

Tanko ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin da yake kare kansa a gaban babbar kotu a Jihar Kano.

Ana tuhumar Tanko mai shekara 34 tare da Hashimu ɗan shekara 37 da kuma Fatima Musa mai shekara 26, dukkan su mazauna Tudun Murtala a gaban babbar kotun.

Ana tuhumar su da laifuka 5 da suka haɗa da yunƙurin garkuwa da mutum, garkuwa da mutum, haɗin baki, ɓoye gawar Hanifa da taimakawa wajen aikata laifin.

A wata shaida da M.L. Usman ya jagoranta, lauyan da ke kare shi, Tanko ya ce shi da mutum biyun da ake tuhuma ba su san yadda Marigayiya Hanifa ta rasu ba.

Ya ce a cikin watan Disambar 2021, ya samu matsala ta kuɗi sosai, don haka ya je banki neman lamuni, amma aka ce masa bai cika sharuɗɗan bayar da irin wannan lamuni ba.

“A ranar 4 ga Disambar 2021, na yanke shawarar in je in ɗauko Hanifa a makarantar Islamiyya a adaidaita sahu, na ɗauke ta, na kai ta gidana da ke Tudun Murtala a Kano.

“Da na isa gida, matata ta tambaye ni ‘yar wane ne, na ce mata ‘yar ɗaya daga cikin ma’aikatana ce da ta yi tafiya, kuma nan da kwana biyu zuwa uku za ta dawo.

“A ranar 10 ga Disamba, 2021, ina kan hanyata ta zuwa kasuwa sai na haɗu da wani Habu, wanda ya nemi aikin gadi a makarantata amma har yanzu ba a ɗauke shi aiki ba.

“Na ce masa Ina da aiki mai sauƙi da zan ba shi, saboda haka ya zo makarantar da ke Tudun Murtala; Na ce masa akwai yarinyar da zai kula mini da ita na kwana ɗaya kacal a cikin harabar makarantar.

“Sai muka yi musayar lambar waya kuma ya yarda ya zo da misalin ƙarfe 11:30 na dare, daga nan muka rabu.

“A wannan ranar da misalin qarfe 10:00 na dare na ɗauke Hanifa daga gida na a lokacin da take barci mai nauyi; nisan gidana zuwa makaranta bai yi nisa ba.

“Hanifa ta kwana a ɗaya daga cikin ofisoshin makarantar a kan kujera kuma na kulle na bar ta a makarantar,” in ji Tanko.

Ya kuma shaida cewar a hanyarsa ta komawa gida ya yi ƙoƙarin kiran Habu ɗin, inda ya ƙara da cewa washegari da misalin ƙarfe 7:30 na safe ya je makarantar, sai ya kaɗu da ganin Hanifa ta na barci kamar yadda ya bar ta.

“Na taɓa hannunta amma ba ta motsa ba,” in ji shi, inda ya shaida wa kotun cewa ya yi wa wanda ake ƙara na biyu ƙarya da ya zo ya binne gawar da ya ɓoye ta a cikin buhu a harabar makarantarsa.

A yayin tuhumar, lauyan masu shigar da ƙara, Antoni-Janar na Jihar Kano, Barr. Musa Abdullahi-Lawan, ya tambayi wanda ake ƙara ko waɗanda ake ƙara na biyu da na uku sun san an sace Hanifa da kuma yadda ta mutu daga baya.

Tanko ya amsa cewa su biyun ba su da masaniyar cewa an yi garkuwa da marigayiyar da kuma yanayin da ya kai ga mutuwar ta.

Alqalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya ɗage cigaba da shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron kariya.

Laifukan da ake tuhumar su Tanko sun sava da sashe na 97, 95 da 273, 274(b) da 277 na kundin laifuffuka na dokokin Jihar Kano, 1991.