Za a shiga wahalar fetur da ba a taɓa yi ba — IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Dillalan Man fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta yi gargaɗin cewa, ‘yan Nijeriya za su ga wahalar man fetur da ba su taɓa ganin irinta ba a ƙasar, idan dai har hukumar mai ta NMDPRA ba ta biya su kuɗaɗen dakon mansu ba.

Shugaban IPMAN na Shiyyar Kano, Bashir Ahmad Ɗan-Malam, shi ne ya yi wannan gargaɗi a taron manema labarai a Kano ranar Litinin.

A cewarsa, rashin biyan kuɗin dakon, wanda a turance a ke kira ‘bridging claims’, wanda adadin sa ya haura Naira biliyan 500, ya sanya da yawa daga cikin dillalan sun durƙushe.

Ya ƙara da cewa rashin biyan kuɗaɗen da NMDPRA ta yi ya sanya wasu ‘yan ƙungiyar sun kasa ma dakon man zuwa jihohin ƙasar nan.

A cewar Ɗan Malam, akwai isashshen mai a defo-defo a ƙasar nan, amma ‘yan ƙungiyar ba za su ci gaba da dakon shi zuwa jihohi ba saboda qin biyan su maqudan kuɗaɗen da ba a yi ba kuma hakan, a cewar sa, ya yi wa kasuwancin su illa.

“Wasu fa bashi ma suka ci na banki suke harkar nan. Waɗannan kuɗaɗen da mu muke tara su domin a samu daidaito wajen farashin man fetur yadda ‘yan ƙasa za su samu sauƙi.

“Mu na da isashshen mai a ƙasa, amma ba za mu iya cigaba da rarrabawa basabo da an ƙi biyan mu kuɗaɗen mu na dako.

“Idan dai ba a biya mu kuɗaɗen nan ba, to ‘yan ƙasa su shirya ganin wahalar man fetur da ba a tava ganin irin ta ba,” in ji Ɗan-Malam.

Ya ƙara da cewa tun sanda a ka kafa NMDPRA a bara, sau biyu ta tava biyan su kuɗaɗen, inda ya koka cewa yanzu suna bin kuɗaɗen na wajen watanni 9.

Bayan ya yaba wa kamfanin mai na NNPC bisa ƙoƙarin tara isashshen man fetur, Ɗan Malam ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya NMDPRA ta biya su kuɗaɗen su domin kawo ƙarshen matsalar a ƙasa baki ɗaya.