Labarai

Gwamnati ta yi wa Magu ƙarin girma duk da zargin rashawa

Gwamnati ta yi wa Magu ƙarin girma duk da zargin rashawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar aikin ‘yan sanda ta tabbatar da ƙarin girma ga tsohon shugaban riƙo na Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya (EFCC), Mustafa Ibrahim Magu zuwa Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, tare da wasu mutane biyar. AIG Magu Ibrahim wanda ke gargarar yin ritaya, shi ne wanda ya fi kowa girma a tsararrakinsa kuma ya ƙasa samun ƙarin girma har sau biyu bayan da ya dawo hukumar ‘yan sanda daga EFCC. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta tabbatar da ƙarin girma ga John Ogbonnaya Amadi a…
Read More
Budurwa ta kai mahaifinta kotun Musulunci bisa ƙin aura mata saurayinta

Budurwa ta kai mahaifinta kotun Musulunci bisa ƙin aura mata saurayinta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata matashiya Halima Yunusa ta kai mahaifinta ƙara Kotun Shari'ar Musulunci a Kaduna kan zargin ƙin aurar mata masoyinta mai suna Bashir Yusuf. Jairdar Daily Trust ta ruwaito cewa Halima ta shaida wa kotun cewa tana matuƙar son Yusuf amma iyayenta sun ƙi yarda su aura mata shi. Mahaifin mai suna Ibrahim ya shaida wa kotun cewa yana sane da irin soyayyar da ke tsakanin 'yarsa da Yusuf, amma a cewarsa, Yusuf bai kammala cika duka sharuɗan aure ba. Mahaifin ya yi ikirarin cewa ya faɗa wa saurayin 'yarsa da ya turo iyayensa amma…
Read More
Babu ranar janyewa daga yajin aiki, cewar ASUU

Babu ranar janyewa daga yajin aiki, cewar ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun ce an kasa cimma matsaya tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’oi ASUU da Gwamnatin Tarayya, kan yajin aikin da ƙungiyar ta shafe matanni tana yi. Tun watan Fabrairun 2022 ASUU ta shiga yajin aiki, haka ma ƙungiyar ma’aikatan jami’a sun shiga nasu yajin aikin daga baya kan wasu buƙatu da ƙungiyoyin suke son gwamnati ta cika masu. Rahotanni sun ce ɓangarorin sun tattauna a ƙarshen mako, amma babu wata matsaya da aka cimma tsakanin shugabannin ƙungiyar malaman ASUU da ƙungiyar SSANU da NASU da kuma ɓangaren gwamnati, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Shugabannin…
Read More
‘Yan ta’adda sun sace jami’in kula da harkokin ɗaliban AGP

‘Yan ta’adda sun sace jami’in kula da harkokin ɗaliban AGP

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau. Hukumomin Abdu Gusau Polytechnic Talata Mafara a jihar Zamfara sun tabbatar da sace jami’in kula da harkokin ɗaliban Polytechnic Mal. Sanusi Halilu ta ƙungiyar 'yan ta'adda. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin hulɗa da jama’a na kwalejin kimiyya da fasaha ta HOD mass Communication, Mal. Aliyu Damri (ANIPR), and made available to Blueprint in Gusau Laraba. Sanarwar ta nuna cewa, Mal. An yi garkuwa da Sanusi Halilu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Talata. “Jami’in kula da ɗaliban mu Mal Sanusi Halilu tare da sauran…
Read More
Cikin shekara bakwai, APC ta yi ayyukan da suka gagari PDP

Cikin shekara bakwai, APC ta yi ayyukan da suka gagari PDP

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta samu nasarori da dama fiye da kowace jam'iyya a Nijeriya a shekara bakwai da ta yi tana mulki. Adamu ya bayyana haka ne a wajen taron ƙaddamar a kwamitin tantance 'yan takarar majalisun jihohi a ranar Talata a Abuja. Shugaban jam'iyyar ta bakin wakilcin mataimakinsa na shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya jaddada cewa ba ya kokwanto daukacin 'yan takarar da suka hadu a cibiyar tantancewa za su ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin jam'iyyar. Da yake yi wa 'yan kwamitin…
Read More
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 30 a hanyar Abuja-Kaduna

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 30 a hanyar Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla fasinjoji 30 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata. Wannan lamari dai ya zo ne sa'o'i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da buɗe hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda wasu gungun 'yan bindiga suka daƙile shi, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da mutane da dama a watan Maris ɗin 2022. A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Jirgin Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta sanar da cewa, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin sake dawo…
Read More
BIDIYO: Tashin bom a Kano

BIDIYO: Tashin bom a Kano

Mazauna yankin Sabon Gari a birnin Kano sun kiɗeme sakamakon tashin bom da ya auku a yankin a safiyar Talata. Yazuwa wallafa wannan bidiyon ba a tantance adadin mutanen da fashewar ta rutsa da su ba.
Read More
Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: Mahara sun sako mai juna-biyu

Harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna: Mahara sun sako mai juna-biyu

Daga BASHIR ISAH 'yan bindiga sun sako wata mata mai juna-biyu tare da wasu daga mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna wanda ya auku lokutana baya. Manhaja ta gano cewa maharan sun sako matar ne bisa ganin damarsu. Hoton bidiyon matar da lamarin ya shafa ya yi ta karakaina a soshiyal midiya inda aka ga matar sanye baƙin hijabi da baƙin abin rufe baki da hanci. Tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da daidaita da maharan domin a sakon ragowar mutanen da ke hannunsu. Ta ce lamarin abin damuwa ne matuƙa saboda…
Read More
Almundahana: Akanta-Janar, Ahmed Idris ya faɗa a komar EFCC

Almundahana: Akanta-Janar, Ahmed Idris ya faɗa a komar EFCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar EFCC ta cika hannu da Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati. Majiyarmu ta nuna Idris ya faɗa a komar jami'an EFCC ne da yammacin Litinin a Kano sannan suka ɗauke shi zuwa Abuja don ya amsa musu tambayoyi. Majiyar ta ce kafin wannan lokaci da ma EFCC na bincike kan batun karkatar da biliyan N80 mallakar gwamnati da aka zargi Idris da aikatawa ta hanyar amfani da wasu kwantiragi. Sakamakon bincike ya nuna kamfanonin da aka yi amfani da su wajen aiwatar da kwantiragin na da nasaba…
Read More
APC ta saka ranar da za ta tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa

APC ta saka ranar da za ta tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta sakar ranar 23 ga Mayu a matsayin ranar da za ta tantance masu sha'awar taka yin takara a jam'iyyar a babban zaɓen 2023 mai ƙaratowa. Sakataren Tsare-tsare na Jam'iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Suleiman Arugungun shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, jim kaɗan bayan rantsar da shuwagabanni da sakatarorin kwamitin tantance 'yan majalisun tarayya, sanatoci da kuma na 'yan takarar gwamna. Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa Jam'iyyar APC za ta yi zaven fidda gwani na…
Read More