Labarai

Abdulkareem Abubakar ya zama Garkuwan Sarkin Dawakin Bajoga

Abdulkareem Abubakar ya zama Garkuwan Sarkin Dawakin Bajoga

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Sarkin Dawakin Sarkin Bajoga Alhaji Bello Adamu ya naɗa masu sarautun gargajiya 18 ciki har da Sufeton 'yan sanda, Abdulkareem Abubakar a matsayin garkuwansa. A lokacin bikin naɗin sarautar, Sa'in Funakaye Alhaji Umar Abdulsalam Baciji, ya yaba wa Sarkin Dawakin Bajoga na yadda ya zaɓo haziƙan matasa 'yan Boko da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati ya ba su sarautu daban-daban don ciyar da masarauta gaba. Sa'in Funakaye, ya ce hakan zai ƙara wa masarauta da sarakuna wanda sune ke da jini a jiki da za su iya gudanar da duk abinda ake so akan…
Read More
Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da zargin cinye alawus ɗin ƙananan sojoji

Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da zargin cinye alawus ɗin ƙananan sojoji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da wani zargi na cin hanci da rashawa da wasu manyan sojojin ke yi. Sojojin sun yi kukan cewa manyansu na cinye musu kuɗaɗensu na alawus, inda suka buƙaci Shugaba Buhari ya ɗauki mataki a kai, idan ba haka ba za su yi bore. Jami'an sun zargi manyansu da cinye musu kuɗaɗensu na alawus. Rundunar sojin ta bayyana cewa tana aiki ne da tsarin biyan albashi na bai-ɗaya ta intanet da gwamnati ta fito da shi, kuma abin da take yi ba shi da bambanci da wanda takwarorinta,…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi

Daga BASHIR ISAH Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Hon Baba Shehu a kan hanyarsa ta komowa Keffi daga Lafia babban birnin jihar Nasarawa. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma'a inda maharan suka yi awon gaba da Shugaban Karamar Hukumar tare da direbansa, Mohamme Tanimu (Senior Man). Sai dai dogarin Shugaban Karamar Hukumar, Alhassan Habeeb, ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga yayin harin. Da safiyar Asabar aka yi jana'izar marigayi Habeeb a Keffi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada. Ya zuwa haɗa wannan labari, maharan sun buƙaci a biya su miliyan N30 kafin su…
Read More
2023: Atiku ya yi alƙawarin sake fasalin Nijeriya

2023: Atiku ya yi alƙawarin sake fasalin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana shirinsa na sake fasalin Nijeriya domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da tsaro, idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa. Atiku, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da wakilan zave na jam’iyyar PDP a  Lahadin makon nan a Abiya, ya ce zai kawo sauyi a ƙasar idan aka ba shi dama. Ya ce indai 'yan ƙasa suna so su cimma muradun su, akwai buƙatar jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaɓen 2023. Ɗan…
Read More
EFCC ta kama Akanta Janar na Nijeriya, Ahmed Idris

EFCC ta kama Akanta Janar na Nijeriya, Ahmed Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na Nijeriya bisa zarginsa da almundahana ta Naira biliyan 80. Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022. Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi. EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja. An kama Idris bayan ya ƙi karɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika…
Read More
’Yan bindiga sun kashe bakwai da yin garkuwa da dagaci a Kano

’Yan bindiga sun kashe bakwai da yin garkuwa da dagaci a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin ƙauyen Ƙarfi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano tare da kashe aƙalla mutum bakwai da raunata mutum 3 a yayin harin. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta fara farautar waɗannan 'yan bindiga. A ranar Laraba wani ɗan jarida a ƙauyen Sale Hussaini ya ce mahara ɗauke da muggan makamai sun afka ƙauyen da misalin ƙarfe 11 daren Asabar inda suka zarce kai tsaye zuwa gidan Dagaci Abdul-Hayatu Ilu suka waske da shi. Hussain ya ce ɗaya daga cikin mutum…
Read More
Kotu ta dakatar da shugabanncin PDP ɓangaren Sagagi a Kano

Kotu ta dakatar da shugabanncin PDP ɓangaren Sagagi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU Kano Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyyar PDP, ƙarƙashin jagorancin Shehu Wada Sagagi har sai ta gama sauraron ƙarar da aka shigar a gabanta. Ana zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.Wani Bello Bichi ne dai ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi, inda ya yi ƙarar jami’yyar PDP da hukumar INEC da kuma sauran mutane 40. Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin guje wa wani yanayi da za a zama babu…
Read More
Zambar Intanet: Kotu ta tura mutum biyar gidan yari a Edo

Zambar Intanet: Kotu ta tura mutum biyar gidan yari a Edo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata kotu a Jihar Edo ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin Benin. Tun daga farko hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC ce ta kai mutanen ƙara bisa zarginsu da amfani da intanet wurin aikata zamba cikin aminci. Waɗanda aka aika gidan yarin sun haɗa da Amogie Julius da Omogbon Friday Harry da Osaze Okoro da Lucky Tegiri da kuma Omokhua Destiny. Duka Waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa inda cikin laifukan har da batun…
Read More
Mayaƙan IPOB sun ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukuma a Anambara

Mayaƙan IPOB sun ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukuma a Anambara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Anambara ta tabbatar da ƙona shalkwatar Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa da ke Ogidi a jihar Anambra a safiyar Litinin. DSP Tochukwu Ikenga, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ta wayar tarho a Awka. Ya ce maharan, waɗanda ake zargin mambobin haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne, sun kai harin kan shelkwatar Ƙaramar Hukumar da misalin ƙarfe 2 na daren Litinin. Ikenga ya ƙara da cewa haɗin gwiwa da sauran jami’an…
Read More
Deborah: Yadda aka kai waɗanda ake zargi da kisan ɗalibar kurkuku

Deborah: Yadda aka kai waɗanda ake zargi da kisan ɗalibar kurkuku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata kotun majistire da ke Sakkwato ta tura mutanen nan biyu da aka kama da ake tuhuma dangane da kisan ɗaliba Deborah Samuel gidan gyarar hali. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ce ta kama matasan biyu ranar Alhamis 12 ga watan Mayu, a lokacin da ɗalibai suka kashe Deborah Samuel kuma suka ƙona ta akan zargin ta yi ɓatanci ga fiyayyen halitta. A ranar Litinin 16 ga Mayu ce aka gurfanar da matasan biyu: Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunci, waɗanda ɗalibai ne a kwalejin koyar da malanta ta Shehu Shagari. Sai dai bayan da aka…
Read More