Labarai

Kwanaki kaɗan kafin zaɓen fidda gwani na APC, EFCC ta mamaye gidan Okorocha

Kwanaki kaɗan kafin zaɓen fidda gwani na APC, EFCC ta mamaye gidan Okorocha

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a yau Talata sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan jami'an da ake zargin sun zo ne ba tare da sammacin kame ba, sun dage cewa za su tafi da shi da ƙarfi, kamar yadda wani mai taimaka wa Sanatan Imo ta Yamma ya bayyana. Okorocha wanda yana cikin 'yan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC ya fuskanci matsaloli da dama da doka, ko dai daga hukumar EFCC ko kuma wanda ya gaje…
Read More
Miji ya shaida wa kotu: Ba zan iya cigaba da jure dukan matata ba

Miji ya shaida wa kotu: Ba zan iya cigaba da jure dukan matata ba

Wani manomi mazaunin Ibadan, Williams Famuyibo ya roƙi kotun al’ada ta Mapo Grade ‘A’ da ke Ibadan ta raba aurensa da matarsa ​​Sola, sakamakon irin azabar da ya ke fuskanta a hannunta. Famuyibo ya ce, ba zai iya jurewa dukan tsiya daga matarsa ​​ba. Ya ce, “ya mai shari'a, saboda rashin samun kwanciyar hankalin da na ke fuskanta a gida na, ina neman a raba ni da matata”. “A gaskiya, ba ni da kwanciyar hankali domin ba ta kula da ni. Ba zan iya cigaba da jurewa duka daga Sola ba.“Ina da ’ya’ya biyar kafin na auri Sola a shekarar…
Read More
Da Ɗumi- ɗumi: Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha ƙawayan

Da Ɗumi- ɗumi: Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha ƙawayan

Daga BASHIR ISAH Bayanan da Manhaja ta kalato na nuni da cewa, jami’an hukumar EFCC sun yi wa gidan tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Okorocha da ke Abuja ƙawanya. Naija News ta ruwaito cewa, baya ga jami’an EFCC haka nan, an ga ‘yan sanda a wajen ɗauke da bindigogi. Majiya da ga EFCC ta ce kafin wannan lokaci, hukumar ta gayyaci Okorocha sau da dama domin ya amsa mata tambayoyi masu alaka da zargin almundahana amma ya ƙi amsawa. Ya zuwa haɗa wannan labari ba a ji komai ba daga bakin kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, kan batun. Idan dai za…
Read More
Almundahana: Gwamnati ta naɗa muƙaddashin Akanta-Janar

Almundahana: Gwamnati ta naɗa muƙaddashin Akanta-Janar

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta amince da naɗinMr. Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin wanda zai ci gaba da riƙon ofishin Akanta-Janar na Tarayya biyo bayan binciken da EFCC ke kan gudanarwa kan Akanta-Janar, Ahmed Idris bisa zargin almundahana. Hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Sakataren Ma'aikatar Kuɗi da Tsare-tsare na Tarayya, Aliyu Ahmed ya sanya hannu mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Mayu, 2022. Wasiƙar ta ce naɗin zai yi aiki ne ya zuwa lokacin da bikin zai kammala. Kafin wannan lokaci, Nwabuoku darakta ne a Ofishin Akanta-Janar, inda yanzu ya zama mai kula da ofishin na…
Read More
Ƙungiyar 13×13 Movement ta raba buhunhunan shinkafa da masara

Ƙungiyar 13×13 Movement ta raba buhunhunan shinkafa da masara

Daga AMINA YUSUF ALI a KANO Shugaban ƙungiyar 13x13 Movement na ƙasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya jagoranci raba kayan abinci: Buhunhunan shinkafa da buhunhunan masara wanda ƙungiyar (Buhari For All) ta bai wa ƙungiyar 13x13 Movement kyautar su. Shi kuma shugaban ƙungiyar, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ne ya jagoranci rabawa. An ba wa kowanne mutum ɗaya buhunan shinkafa uku-uku da buhunhunan masara guda hur-huɗu. Sannan aka ɗora masa kuɗi Naira 20,000 ga kowanne mamba da ke cikin ƙungiyar ta 13x13 Movement. Mambobin ƙungiyar 13x13 Movement sun yi wa ƙungiyar Buhari For All godiya tare da…
Read More
An samu sabbin nutane 169 da suka kamu da COVID-19 a babban yankin Sin

An samu sabbin nutane 169 da suka kamu da COVID-19 a babban yankin Sin

Daga CMG HAUSA Bisa alƙaluman da hukumar kula da lafiyar ƙasar Sin ta fitar sun nuna cewa, an samu mutane 169 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a babban yankin ƙasar a ranar Asabar. Daga cikin adadin, 157 na da alaƙa da yada cutar a cikin gida, sannan 12 kuma daga ƙetare. An samu jimillar sabbin kamuwa da cutar 729 waɗanda ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba a ranar Asabar, yayin da adadin majinyatan da ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba 37,636 suke ƙarƙashin kulawar jami’an kiwon lafiya. Kawo yanzu, adadin mutanen da aka…
Read More
Na samu Jihar Kano a mawuyacin halin tsaro – CP Sama’ila Dikko

Na samu Jihar Kano a mawuyacin halin tsaro – CP Sama’ila Dikko

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Sama'ila Dikko, ya bayyana cewa ya samu Jihar Kano cikin mawuyacin halin tsaro, amma zuwan sa sun haɗa kai da masu ruwa da tsaki sun shawo kan lamarin. Da yake ƙarin haske ga wakilin Manhaja a makon jiya, dangane da yadda ya samu Jihar ta Kano a matsayin Kwamishinan 'Yan Sanda, ya ce lallai ya samu jihar a wani hali na ƙuncin rashin tsaro ta fuskoki daban-daban, amma kuma bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zama da sauran jami'an 'yan sandan da ɓangarorin da ya kamata don ƙara…
Read More
Za mu ci gaba da kawo sauyi ta fuskar kasuwanci a Jihar Kano – Shugaban Alkamatu

Za mu ci gaba da kawo sauyi ta fuskar kasuwanci a Jihar Kano – Shugaban Alkamatu

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Shugaban Kamfanin Alkamatu a Jihar Kano, Kwamared Alkamatu Abdulkadir ya ce za su cigaba da kawo sauhe-sauye masu ma'ana ta fuskar kasuwanci a Jihar Kano. A ci gaba da wayar wa da matasa da al'ummar Jihar Kano da suke yi dangane da muhimmancin dogaro da kai ta fuskar kasuwanci da matakin da ya kamata a ce al'umma sun bi wajen ganin sun zama masu dogaro da kansu da kamfanin Alkamatu ke ta fafutukar yi ga al'ummar jihar Kano, Alkamatu ya buƙaci sahalewar gwamnati da masu hannu da shuni kan ƙara zuwa don zuba hannu…
Read More
Allah ya yi wa Hajiya Rabi’atu Safiyanu Ahmad rasuwa

Allah ya yi wa Hajiya Rabi’atu Safiyanu Ahmad rasuwa

Daga WAKILINMU Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a kan hanyarta ta zuwa Yola daga Kaduna don halartar Musabaƙar RABIDA. Kafin rasuwarta, marigayiyar ita ce Amirar Gidauniyar Nana Asma'u ta Ƙasa kuma shugabar Ƙungiyar IMWON. A halin rayuwarta, Hajiya Rabi'atu ta ba da gudunmawa matuƙa a harkokin da'awa da ayyukan Hajji a matakin jiha da ƙasa. 'Yan uwa, dangi, maƙwabta da abokan arziki na kusa da nesa na ci gaba da yi wa marigayiyar addu'ar dacewa da Jannatul Firdausi.
Read More