Labarai

Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Nasarawa ta tara Naira biliyan 40 ta sabon tsarin tara kuɗin shigarta

Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Nasarawa ta tara Naira biliyan 40 ta sabon tsarin tara kuɗin shigarta

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga na cikin gida wato Nasarawa State Internal Revenue Services, Ahmed Muhammad, ya bayyana cewa hukumar a ‘yan kwanakin baya ta taro kuɗaɗen shiga da sun kai kimanin Naira biliyan 40 sakamakon ƙirƙiro da sabon tsarin tattaro kuɗaɗen shiga da ta yi kwanakin baya wato na yin amfani da mashinan zamani don samun sauƙin karɓan kuɗaɗen haraji a jihar. Ahmed Muhammed ya sanar da haka ne a lokacin da yake zanta da wakilin mu dangane da harkokin hukumar a ofishin sa dake Lafiya babbar birnin jihar ranar Litinin 23 ga…
Read More
Hukumar NUDB ta yi gargaɗin a riƙa bin ƙa’idojin mallakar filaye da gine-gine a biranen Jihar Nasarawa

Hukumar NUDB ta yi gargaɗin a riƙa bin ƙa’idojin mallakar filaye da gine-gine a biranen Jihar Nasarawa

•Ta ce za ta cigaba da rushe gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar Tsara Manyan Birane na Gwamnatin Jihar Nasarawa, wato Nasarawa State Urban Development Board (NUDB) a turance, ta gargaɗi al’ummar jihar baki ɗaya dangane da mallakar filaye ko yin gine-gine ba bisa ƙa’ida ba a manyan biranen jihar. Manajan daraktan hukumar, Injiniya Idris Wada ne yayi wannan gargaɗi a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishin sa dake babbar hedikwatar hukumar a Lafiya babban birnin jihar ranar Litinin 23 ga watan Mayun shekarar 2022 da ake ciki.…
Read More
Kuskure ne saka sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya, inji Sarkin Dutse

Kuskure ne saka sarakuna a tsarin mulkin Nijeriya, inji Sarkin Dutse

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji (Dr.) Nuhu Muhammad Sunusi, ya ce kuskure ne sama wa sarakuna matsayi a cikin tsarin dokokin ƙasa kamar yadda majalisar ƙasa ta yi yunƙurin yi kwanan baya. Sarkin ya ce ya ji daɗin yadda ƙudirin ya faɗi bai kai ga samun nasara ba a Zaure Majalisar Nijeriya a lokacin da aka tafka mahawa akan lamarin. Sakin ya faɗi haka ne a lokacin da ya amshi baƙuncin shugaban majalisar dokoki ta Nijeriya Sanata Ahmed Lawan a fadarsa da ya kawo masa ziyarar bangirma tare da neman goyan bayansa akan buƙatarsa…
Read More
Matsalar tsaro: Sama da Katsinawa 13,000 suka yi hijira zuwa Nijar – Gwamna Masari

Matsalar tsaro: Sama da Katsinawa 13,000 suka yi hijira zuwa Nijar – Gwamna Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa al’ummar Jihar Katsina sun ga bala’in ‘yan bindiga, a cikin mummunan tashin hankalin da aka shiga matsananciyar wahala. Masari ya ce bala’i ya yi tsananin da an fatattaki mutane daga yankunansu, har ta kai sama da Katsinawa 13,000 sun yi gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar. Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da ‘yan bindiga suka hana zaman lafiya. Masari na magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda ya je a matsayin sa na ɗaya daga cikin ‘yan takarar…
Read More
Masu buƙata ta musamman sun yi barazanar kai ƙarar INEC kotu

Masu buƙata ta musamman sun yi barazanar kai ƙarar INEC kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu buƙata ta musamman a jihar Ekiti da ke Kudancin Nijeriya sun yi barazanar kai hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan ƙorafin ƙin tanadar abubuwan da suke buƙata domin shiga zaɓen gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni. Jaridar Premium Times ta ambato shugaban ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen jihar Ekiti, David Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa matuƙar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da ƙara kotu kan take haƙƙinsu, da dokokin Nijeriya suka ba su a…
Read More
Boko Haram sun kashe mutane 40 a Borno

Boko Haram sun kashe mutane 40 a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mayaƙan Boko Haram sun kashe farar hula 40 a Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno a Arewa maso gabashin Nijeriya. Ƙungiyar Boko Haram su na ci gaba da ta'asa jifa-jifa duk da kassara ta da hukumomin Nijeriya suka ce sun yi. Rahotanni sun ce ɗimbin ‘yan ta’adda ne suka yi wa farar hula da ba su ɗauke da makami ƙawanya, inda suka yi ta yi musu yankan rago a ranar Lahadi. ‘Yar majalisar wakilai ta Tarayyar Nijeriya da ke wakiltar mazaɓar, Zainab Gimba ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari. Wata majiya…
Read More
Kisan IPOB: Mijin Harira ya koma Adamawa bayan samun tallafin dubu N500 daga Gwamna  Soludo

Kisan IPOB: Mijin Harira ya koma Adamawa bayan samun tallafin dubu N500 daga Gwamna Soludo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mijin matar da aka yi wa kisan gilla tare da 'ya'yanta huɗu a Jihar Anambra, Jibril Ahmed, ya tattara komatsansa ya bar jihar ya koma Jihar Adamawa da zama. Haka kuma Gwamnan Jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya bai wa magidancin tallafi na N500,000 domin rage raɗaɗin ibtila'in da ya auku gare shi. Da yake yi wa manema labarai bayani, Jibril Ahmed ya ce shi ɗan asalin Adamawa ne, kuma ya ɗauki matakin komawa Adamawar ne domin ya fara sabuwar rayuwa saboda a yanzu shi kaɗai ne ya rage bayan da tsegerun IPOB suka…
Read More
An yi kisa a wurin zaɓen fitar da gwani na PDP a Bayelsa

An yi kisa a wurin zaɓen fitar da gwani na PDP a Bayelsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin Nijeriya, Douye Diri, ya yi Allah wadai da kisan wani mutum mai suna Michael Isaiah. Lamarin ya faru lokacin da jam'iyyar hamayya ta PDP ke gudanar da zaɓen fidda gwani na 'yan takarar kujerun majalisa a mazaɓar Ogbia da ke garin a Ƙaramar Hukumar Ogbia. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kola Oredipe, ya rattava wa hannu ya ce ɓatagari ne suka yi kisan domin tayar da zaune tsaye da haddasa tashin hankali a zaɓen fidda gwanin da aka yi a jihar. Gwamnan…
Read More
Jarman Hadejia, Alhaji Abba Sambo ya kwanta dama

Jarman Hadejia, Alhaji Abba Sambo ya kwanta dama

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Aal'ummar masarautar Haɗejia sun tashi a cikin yanayi na jimami a ranar Talata biyo bayan rasuwar Jarman Haɗejia, Alhaji Abba Sambo. Alhaji Abba Sambo Dattijo ne mai shekaru sama da 70 a duniya wanda ya shafe shekaru masu yawa yana kan karagar mulki tun bayan rasuwar mahaifinsa. Marigayin ya yi fama da ciwon koda wanda haka tasa ake masa wankin ƙoda a Asibitin Kwararru na AKTH. Bayan dawo da shi Haɗejia cikin wannan makon ya ci gaba da karɓar magani a Babban Asibitin Haɗejia, inda a ranar Talata ya ce ga garinku nan. An yi masa…
Read More
Dubun wasu masu garkuwa ta cika a Kaduna

Dubun wasu masu garkuwa ta cika a Kaduna

Daga WAKILINMU Jami’an Sashen Binciken Sirri na Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya (IRT), sun damƙe wasu ’yan ta’adda biyu bisa zargin yunƙurin garkuwa da fyaɗe a Jihar Kaduna. Abdurahman Lolo da Muhammed Sani sun shiga hannu ne a yankin Bandoko bayan da suka shiga gidan wani magidanci suka yi garkuwa da shi. Kakakin 'yan sandan Jihar Kaduna, CSP Muyiwa Adejobi, ya ce waɗanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun yi shirin su yi garkuwa da magidancin sannan kuma su yi wa mai ɗakinsa fyade. Tawagar jami’an ƙarƙashin jagorancin DCP Olatuniji Disu, sun samu nasarar cafke waɗanda ake…
Read More