Daga WAKILINMU
Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a kan hanyarta ta zuwa Yola daga Kaduna don halartar Musabaƙar RABIDA.
Kafin rasuwarta, marigayiyar ita ce Amirar Gidauniyar Nana Asma’u ta Ƙasa kuma shugabar Ƙungiyar IMWON.
A halin rayuwarta, Hajiya Rabi’atu ta ba da gudunmawa matuƙa a harkokin da’awa da ayyukan Hajji a matakin jiha da ƙasa.
‘Yan uwa, dangi, maƙwabta da abokan arziki na kusa da nesa na ci gaba da yi wa marigayiyar addu’ar dacewa da Jannatul Firdausi.
