Daga CMG HAUSA
Rahotanni daga bikin tallata ranar kasancewar halittu daban-daban na duniya na shekara ta 2022 wanda aka yi a jiya Jumma’a a ƙasar Sin sun ce, ƙasar za ta gaggauta raya tsarin lambunan shan iska da lambunan tsirrai, kuma a shekarar da muke ciki, za ta ƙara gina wasu lambunan shan iska, da kammala tsara shirin raya lambunan tsirrai na ƙasa.
Babban taken ranar kasancewar halittu daban-daban na duniya a bana shi ne, raya halittu masu kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. Sakamakon ƙoƙarin da aka yi na tsawon shekaru, ƙasar Sin ta riga ta gina tsarin kiyaye muhalli, dake ƙunshe da lambunan shan iska da yankunan kiyaye muhallin halittu da sauransu, al’amarin da ya sa ta kiyaye nau’ikan muhallan halittu na ƙasa sama da kaso 90 bisa dari, da kaso 71 bisa ɗari na dabbobi da tsirrai masu darajar gaske a ƙasar.
Fassarawa: Murtala Zhang