Wang Wenbin ya amsa tambayoyin manema labarai game da goyon-bayan da aka nunawa matsayin ƙasar Sin kan batun Taiwan a wajen taron WHO

Daga CMG HAUSA

Za a gudanar da babban taro karo na 75 na hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Mayun bana. Hukumomin kula da harkokin wajen yankin Taiwan sun nuna rashin jin daɗin game da rashin samun gayyatar halartar taron.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Wenbin ya ce, Sin ƙasa ce ɗaya tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar ƙasar Sin halastacciyar gwamnati ce ɗaya kaɗai dake wakiltar ƙasar. Taiwan kuma, wani ɓangare ne da ba za’a iya ware shi daga babban yankin ƙasar Sin ba. Ya ce ya kamata a daidaita batutuwan da suka shafi shigar yankin Taiwan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da WHO, bisa manufar kasancewar ƙasar Sin daya tak a duniya.

Daga shekara ta 2009 zuwa ta 2016, duba da yadda dukkan gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan suka girmama manufar kasancewar ƙasar Sin daya tak a duniya, ƙasar Sin ta yi shiri na musamman don halartar yankin Taiwan babban taron WHO. Amma tun bayan da jam’iyyar DPP ta kama mulkin yankin, ya zuwa yanzu, tana yunƙurin balle yankin daga cikin ƙasar Sin, kuma ba ta amince da manufar kasancewar ƙasar Sin daya tilo a duniya ba, al’amarin da ya kawar da tushen siyasa na halartar yankin Taiwan babban taron WHO.

Gwamnatin Ƙasar Sin tana matukar maida hankali kan zaman lafiya da rayuwar al’ummar Taiwan, kuma bisa tushen manufar kasancewar ƙasar Sin daya tak a duniya, gwamnatin ƙasa ta kan shiryawa Taiwan damammakin halartar harkokin kiwon lafiyar duniya. Wasu maganganun dake cewa, wai rashin halartar yankin Taiwan taron WHO, zai kawo cikas ga cika tsarin kandagarkin yaɗuwar annobar COVID-19 a duniya, ƙarya ce zalla.

Irin wannan ƙudirin gwamnatin ƙasar Sin ya samu goyon-baya da fahimta sosai daga wajen ƙasa da ƙasa, inda kawo yanzu ƙasashe kusan 90, sun gabatar da saƙo zuwa ga hukumar WHO, don shaida matsayinsu na tsayawa kan manufar kasancewar ƙasar Sin daya tak a duniya, da adawa da halartar yankin Taiwan babban taron WHO.

Mai fassara: Murtala Zhang