Sin ta yi kira da a daidaita batun ‘yan guudun hijira yadda ya kamata

Daga CMG HAUSA

Mataimakin wakilin dindindin na ƙasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, ya dace a daidaita batun ‘yan gudun hijira daga dukkan fannoni kuma yadda ya kamata, kana, ya zama dole a kawar da nuna bambanci da fin ƙarfi kan ‘yan gudun hijira, da daidaita sabani ta hanyar siyasa.

Dai Bing ya bayyana a wajen muhawarar dandalin tattauna batun ‘yan gudun hijira na ƙasa da ƙasa karo na farko, cewa, babban dalilin da ya jawo matsalar ‘yan gudun hijira shi ne, rashin daidaiton ci gaba.

Don haka ya ce, ya dace a daidaita matsalar ta hanyar samar da ci gaba. Ya ce ya kamata ƙasa da ƙasa su haɓaka haɗin-gwiwa, da taimakawa ƙasashen ‘yan gudun hijira raya tattalin arziki, da kyautata rayuwar al’umma, da inganta ƙwarewa. Sa’annan su kuma ƙasashen da suka karbi ‘yan gudun hijirar, su ƙara nuna hakuri, don taimaka musu jin dadin rayuwa a ƙasashen.

Mai fassara: Murtala Zhang