PSG ta yi wa Real Madrid yankan baya ta cigaba da riƙe Mbappe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar PSG a ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya yanke hukuncin cigaba da zama a ƙungiyar bayan kwashe makonni ana danganta shi da tafiya ƙungiyar Real Madrid ta ƙasar Spain.

Jaridar L’Equip da ke Faransa da Marca da ke Spain sun ruwaito cewa, Mbappe ya yanke hukucin zama a PSG da kuma rattaba hannu akan wata sabuwar kwangilar shekaru 3 idan wa’adin kwangilar sa ta yanzu ta ƙare a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.

Wakilan Mbappe sun ƙi yin bayani akan sabuwar kwangilar da PSG za ta ba shi, sai dai wasu rahotanni sun ce ƙungiyar za ta yi bayani dangane da yarjejeniyar da ta ƙulla da ɗan wasan lokacin karawar da za su yi da ƙungiyar Metz a parc des Princes yammacin yau.

Batun sauya sheƙa ko kuma cigaba da zaman Mbappe a ƙungiyar PSG ya daɗe yana ɗauke hankalin magoya bayan ƙungiyar da kuma na Real Madrid wadda ta lashi takobin ɗaukarsa a ƙarshen wannan kakar mai ƙarewa.

Shima ɗan wasan bai taɓa ɓoye sha’awar san a komawa ƙungiyar Madrid ba, amma PSG tayi iya bakin ƙoƙarin ta wajen shawo kan sa domin sake tunani akai.

Wannan matsayi ya nuna cewar Mbappe zai cigaba da zama a PSG tare da Neymer da Lionel Messi domin taimakawa ƙungiyar a yunƙurin ta na ganin ta lashe kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Jaridar Marca ta Spain ta ruwaito cewa, Mbappe ya shaida wa shugaban Real Madrid Florentina Perez shawarar da ya yanke na cigaba da zama a PSG.