Babu tsawaita jaddawalin INEC!

A kwanakin baya ne shugaban majalisar ba da shawara ta jam’iyyun siyasar Nijeriya (IPAC), Yabagi Sani ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta ƙara wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasar Nijeriya.

A yayin da ya ke yin wannan kiran, ya ce, matsalar shiyya-shiyya da canjin mulki ya mamaye tattaunawar da jam’iyyun siyasa ke yi wanda ya sa ya zama dole a tsawaita wa’adin ta yadda jam’iyyun za su yi aiki sosai.

Ya ƙara da cewa, da wannan ne jam’iyyu za su iya gudanar da ayyuka masu ɗaukar lokaci kamar tuntuɓar juna, wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, da yaƙin neman zaɓe, don haka akwai buƙatar INEC ta ƙara lokaci.

A cewarsa, IPAC bayan kammala tantance jadawalin INEC da wasu batutuwan da suka shafe su, ta cimma matsaya ɗaya na neman tsawaita kwanaki talatin da bakwai (37) zuwa wa’adin gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu da kuma kamo bakin zaren rikice-rikicen da suka taso daga zaɓukan.

Bisa la’akari da hakan, shugaban IPAC yana kira ga hukumar ta INEC da ta ƙara wa’adin gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyu da kuma warware rigingimun da suka biyo baya tun daga ranar 3 ga watan Yunin 2022 zuwa ranar 4 ga watan Yuli 2022.

A martanin da ta mayar, INEC ta ƙi amincewa da ƙara wa’adin gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

Idan za mu iya tuna cewa, hukumar ta sake duba jadawalin ta na zaɓen 2023 a Nijeriya a watan Fabrairu bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dokar zaɓe ta 2022.

A bisa bin sabuwar dokar zaɓe, hukumar ta sanya ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga watan Yuni domin zaɓen ’yan takarar jam’iyyun siyasa a zaɓen 2023.

A ra’ayin wannan jarida, ya kamata INEC ta cigaba da bin jadawalinta tare da yin tir da duk wani matsin lamba daga jam’iyyun siyasa.

INEC, a namu ra’ayin, tilas ne ta kiyaye jadawalin lokacinta, kuma ta yi watsi da duk wani yunƙuri na ’yan siyasa su yi amfani da su.

Haƙiƙa, domin ƙasar nan ta samu ƙarfin da ta ke nema, akwai buƙatar a samar da tsare-tsare masu ƙarfi da za su bijire wa ’yan siyasa da suka kware wajen dagewa a kan tafiyarsu ba tare da la’akari da illar da ayyukansu da rashin aiwatar da su zai haifar ga sauran ’yan siyasa da ’yan ƙasa ba.

Misali, zaɓen shugaban ƙasar Amurka yana faruwa ne duk bayan shekaru huɗu a ranar Talata ta farko bayan Litinin ta farko a watan Nuwamba. Ranar tsayayyan rana ce ba tare da la’akari da wanda ke jagorantar hukumar zave ba. Wannan shi ne yadda ya kamata ya kasance.

Abin baƙin ciki shi ne, shugabannin siyasarmu suna wasa da ƙa’idojin ƙasa, kuma koyaushe suna neman duk wata hanyar da za su bi don cimma burinsu na son kai. Wannan ya kamata a daina.

Haka kuma, idan INEC ta amince da buƙatarsu, jam’iyyun siyasa za su yi kira da a ƙara musu tsawaita, har ma su buƙaci a qara wa babban zaɓe.

A ra’ayinmu, jam’iyyun siyasa ba su da dimokuraɗiyyar cikin gida. Wannan rashin iya tafiya bisa ƙa’ida ya yi wa jam’iyyu illa a baya.

Mu tuna yadda a shekarar 2019 wata babbar kotun tarayya da ke Fatakwal, jihar Ribas ta umarci INEC ta soke sunayen ’yan takarar jam’iyyar APC a jihar Ribas a zaɓukan watan Fabrairu da Maris 2019.

Alƙalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya ke yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar gaban kotun, inda ya buƙaci kada ta amince da duk wani ɗan takara daga jam’iyyar APC na jihar.

Alƙalin ya ɗauki wannan matakin ne saboda jam’iyyar ta gudanar da taro guda biyu a layi ɗaya.

Haka lamarin ya kasance a garin Zamfara lokacin da kotuna ta kori dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC saboda sun ƙi bin ƙa’ida.

Jerin laifuka na jam’iyyun siyasa yana da yawa. Dole ne jam’iyyun siyasa su koyi mutunta wa’adin da INEC ta tanada, kuma bai kamata ya kasance akasin haka ba. Kada a sanya INEC ta shiga cikin shirye-shiryen jam’iyyun. Muna ganin cewa bai kamata hukumar ta kasance a hannun ’yan siyasa ba.

Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, muna kira ga INEC da ta tsaya tsayin daka kan matakin da ta ɗauka na ƙin tsawaita lokacin gudanar da zaɓe. Mun yi imani da cewa wata ɗaya ya isa ga masu neman zaɓen wakilai na zaɓen fidda gwani. Don haka, ya kamata gudumar hukumar ta faɗa kan duk jam’iyyar da ta kasa cika wa’adin.