Kotun Kano ta yanke wa matashi hukuncin kisa sakamakon garkuwa da kashe yaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun jiha mai lamba 5 da ke zamanta a Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Usman Na-Abba, ta yanke wa wani matashi, Ibrahim Ahmad Khalil hukuncin kisa sakamakon yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara 5 da haihuwa.

Tun da fari dai kotun ta ce ta samu Khalil da laifin garkuwa da yaron, mai suna Ahmad Ado, kuma ɗan ‘yar uwarsa ne, ya kuma kashe shi.

Khalil dai ya ɗauke Marigayi Ado a unguwar Karkasara da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a 2019,  ya kuma nemi Naira miliyan 20 kuɗin fansa, daga baya kuma aka daidaita da shi a kan Naira miliyan 2.

Sai dai kuma kafin a kai masa kuɗin fansar, sai Khalil ya kashe Ado ta hanyar ba shi kwaya da kuma toshe masa baki da hanci da gam.

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Na-Abba ya zartar wa da wanda a ke ƙarar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun cikakkun hujjoji da lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki ya gabatar a gabanta.

Na-Abba ya ɗaure Khalil shekaru 14 a bisa laifin garukwa da mutane, sai kuma hukuncin kisa sakamakon laifin kisan kai.

Bayan kammala zaman kotun, lauyar wanda ake  ƙara, Barista Aisha Hassan Abdulkadir ta ce za su yi nazari akan hukuncin domin ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *