Labarai

Buhari ya yi na’am da sabon tsarin albashin fansho mafi ƙaranci

Buhari ya yi na’am da sabon tsarin albashin fansho mafi ƙaranci

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yarda a biya masu karɓar fansho da sabon tsarin albashi mafi ƙaranci. Sakatariyar Hukumar Fansho, Dr Chioma Ejikeme, ita ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja a Juma'ar da ta gabata. Jami'ar ta ce da wannan amincewar da aka samu daga wajen Shugaban Ƙasa, an ƙarfafa wa kwamitin PTAD kan ya soma gyare-gyare game da abin da ake biyan masu karɓar fansho domin ya daidaita da sabon tsarin biyan haƙƙoƙin nasu. Ejikeme ta ce sabon tsarin biyan fansho ɗin zai soma aiki ne daga Mayu, 2021. Ta kara da…
Read More
Kadafur ya zama muƙaddashin gwamnan Barno na kwana 21

Kadafur ya zama muƙaddashin gwamnan Barno na kwana 21

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Dokokin Jihar Barno ta amince da buƙatar Gwamna Babagana Umara Zulum inda ya nemi a naɗa mataimakinsa, Umar Usman Kadafur, a matsayin mauƙaddashinsa. Zulum ya miƙa wannan buƙata ga majalisar ne domin ba shi zarafin tafiya hutu na kwana 21, kama daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu, 2021. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdulkarim Lawan, ya ce tun a ranar 23 ga Afrilun da ya gabata gwamnan ya miƙa wa majalisar wasiƙar wannan buƙatar tasa, yana mai neman majalisar ta ba shi damar tafiya hutu na kwanaki 21. Kazalika, Shugaban Majalisar ya ce…
Read More
Gwamnatin Neja ta sauya wa ‘yan gudun hijira 3500 sansani

Gwamnatin Neja ta sauya wa ‘yan gudun hijira 3500 sansani

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Neja ta sake wa wasu 'yan gudun hijira a jihar su 3500 matsuguni zuwa Gwada Model Primary School a Juma'ar da ta gabata. Waɗanda lamarin ya shafa 'yan gudun hijira ne daga yankunan da 'yan fashin daji da Boko Haram suka ɗaiɗaita a jihar kwanan nan. A bayanin Gwamna Sani Bello ta bakin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA), ya bada umarni a tabbatar 'yan gudun hijirar na samun kulawar da ta dace na zaman da za su yi a sabon sansanin nasu har zuwa lokacin da komai zai daidaita kana a maida kowa…
Read More
Jami’ar Edusoko mafita ce ga ɗaliban Neja masu neman gurbin karatu – Gwamna Bello

Jami’ar Edusoko mafita ce ga ɗaliban Neja masu neman gurbin karatu – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya ce kafa Jami'ar Edusoko zai taimaka wajen magance ƙalubalen samun gurbin karatu da ake fama da shi a jihar Neja. Gwaman ya bayyana haka ne sa'ilin da ya karɓi baƙuncin Kwamitin Amintattu na Jami'ar Edusoko ƙarkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, a fadar gwamnatin jihar da ke Minna. Ya ce akwai ɗimbin ɗalibai a jihar Neja da ke neman gurbin karatu a jami'a, yana mai cewa zuwan Jami'ar Edusoko zai zama mafita ga ɗaliban. Baya ga yaba wa Etsu Nupe bisa ƙoƙarin samar da wannan jami'a, Gwamna Bello…
Read More
An cafke ‘yan fashi 6 ɗauke da shanu 183 da kuɗi dubu N268 a Oyo

An cafke ‘yan fashi 6 ɗauke da shanu 183 da kuɗi dubu N268 a Oyo

Daga AISHA ASAS Rundunar tsaro ta musamman a jihar Oyo mai ƙunshe da 'yan bangan OPC da Amotekun da VGN, ta cafke wasu mutun shida da ake zargin 'yan fashin daji ne a safiyar Alhamis da ta gabata ɗauke da shanu 183 a yankin ƙaramar hukumar Kajola ta jihar. A cewar Kwamandan Amotekun na jihar Oyo, Col Olayinka Olayanju (mai murabus), ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a hanyar Okeho zuwa Ilua da kuma hanyar Okeho zuwa Iseyin da misalin ƙarfe 4 na asuba na wannan rana. Kwamandan ya ce sun kama ɓarayin ne bayan ɗauki ba daɗin…
Read More
Majalisa ta yi kumfar baki kan yadda tsaron Nijeriya ya dagule

Majalisa ta yi kumfar baki kan yadda tsaron Nijeriya ya dagule

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana cewa taɓarɓarewar tsaron ƙasa abin kunya ne ga Nijeriya. Majalisar ta bayyana haka ne a zamanta na Talatar da ta gabata, inda sanatoci da dama suka nuna takaicinsu kan mummunan halin da tsaron ƙasa ya faɗa. Sa'ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a muhawarar da aka tafka a zauren Majalisar, Sanata Birma Enagi (APC Neja ta Kudu) ya ce, "Tabbas lamari ya lalace kuma abin kunya ne. Gwamnatin Tarayya ta yi sakwa-sakwa wajen yaƙi da ɓarayin daji da 'yan Boko Haram." Ya ce, "Mafi takaicin abin da ke faruwa shi ne…
Read More
NUJ ta yi kira ga NBC da ta janye tarar milyan 5 da ta ɗora wa tashar Channels

NUJ ta yi kira ga NBC da ta janye tarar milyan 5 da ta ɗora wa tashar Channels

Daga AISHA ASAS Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) ta yi kira ga Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC) da ta tsananta lura game da yadda take ɗaukar mataki a kan kafafen yaɗa labarai a cikin ƙasa. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Chris Isiguzo, ya ce sun yi mutuƙar damuwa da barazanar da hukumar NBC ta yi na dakatar da lasisin tashar talabijin ta Channels saboda tattaunawar da ta yi da mai magana da yawun tsegerun IPOB a wani shirinta da tashar ta gabatar kwanan nan. NUJ ta ce tana buƙatar NBC ta gaggauta janye tarar milyan N5…
Read More
Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona samfurin Johnson & Johnson guda milyan 29.8

Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona samfurin Johnson & Johnson guda milyan 29.8

Daga WAKILINMU Gwamnatin Nijeriya na sa ran ta karɓi allurar rigakafin cutar korona samfurin Johnson & Johnson (J&J) ƙwara milyan 29.8, kamar yadda Dr Faisal Shuaib ya bayyana a Litinin da ta gabata. Shuaib wanda shi ne Daraktan Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na mako-mako da aka saba gudanarwa game da sha'anin yaƙi da cutar korona a Abuja. Ya ce gwamnati ta sanya hannun karɓar rigakafin ne ta Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU), sannan maganin zai shiga hannu ta shirin COVAX ya zuwa ƙarshen Mayu ko farkon Yuni. Jami'in…
Read More
Boko Haram sun karɓe Kaure har sun kafa tutarsu – Gwamna Bello

Boko Haram sun karɓe Kaure har sun kafa tutarsu – Gwamna Bello

Daga AISHA ASAS Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya tabbatar da 'yan Boko Haram sun shigo jihar Neja musamman ma a yankin Kaure da ƙaramar hukumar Shiroro, kuma har ma sun kafa tutarsu. Gwamna Bello ya sanar da hakan ne sa'ilin da ya ziyarci 'yan gudun hijira su sama da 3000 daga yankin ƙaramar hukumar Shiroro da Munya da suka yi sansani a harabar makarantar Firamare ta Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Minna. A cewarsa, "Ina mai tabbatar da cewa akwai ɓurɓushin Boko Haram a Neja, a yankin Kaure. "Na samu bayanin har sun kafa tutarsu a…
Read More
‘Yan bindiga sun raba ƙauyuka 50 da matsugunansu a Neja – Gwamna Bello

‘Yan bindiga sun raba ƙauyuka 50 da matsugunansu a Neja – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce aƙalla ƙauyuka 50 ne 'yan bindiga suka raba da mazauninsu a tsakanin ƙananan hukumomi biyar a jihar, lamarin da a cewar gwamnan ya haifar da rikicin jinƙai a jihar. Gwamna Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake buɗe taron bita na yini biyu kan inganta hanyayoyin tara kuɗaɗen shiga ga ƙananan hukumomi, a garin Minna babban birnin jihar. Gwamnan ya ce akwai buƙatar shirya wannan taro, tare da jaddada buƙatar da ke akwai ƙananan hukumomin jihar su matse ƙaimi wajen tara wa gwamnatin kuɗaden shiga ta…
Read More