21
Jan
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 za a yi zaben gwamnan Jihar Anambara. Hukumar ta bayyana jadawalin ranar zaben da abubuwan da za a aiwatar ne a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Talata a Abuja. Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na hukumar, Mista Festus Okoye, wanda ya bada sanarwar, ya ce hukumar ta yi wani zama a ranar Talata inda ta tattauna kan zaben na Anambara. A cewar sa, za a yi zabubbukan share fage tare da warware duk wani sabani da ka iya…
